Tinubu Ya Dawo Najeriya Daga Faransa, Zai Rantsar da Sabuwar Shugabar Alkalai

Tinubu Ya Dawo Najeriya Daga Faransa, Zai Rantsar da Sabuwar Shugabar Alkalai

  • A yau Juma'a, 23 ga watan Agusta Shugaba Bola Tinubu zai rantsar da Kudirat Kekere-Ekun a matsayin shugabar alkalan Najeriya
  • A wata sanarwa da Cif Ajuri Ngelale ya fitar, ya ce Kekere-Ekun za ta gaji Olukayode Ariwoola, wanda ya yi ritaya daga aiki
  • Rahotanni sun bayyana cewa shugaban kasa Tinubu ya dawo gida Najeriya bayan wata gajeriyar ziyarar da ya kai a kasar Faransa

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - An ruwaito cewa Shugaba Bola Tinubu ya dawo Abuja bayan wata gajeriyar ziyara da ya kai kasar Faransa.

Bayan dawowar shugaban kasar ne ake sa ran zai rantsar da Mai shari’a Kudirat Kekere-Ekun a matsayin sabuwar shugabar alkalan Najeriya.

Kara karanta wannan

Bayan saka ranar zanga zanga ta 2, Tinubu zai gana da matasa a Najeriya

Tinubu zai rantsar da Kekere-Ekun matsayin shugabar alkalan Najeriya
Tinubu ya dawo Najeriya, zai rantsar da Kekere-Ekun matsayin shugabar alkalai. Hoto: @njcNig
Asali: Twitter

Bola Tinubu zai rantsar da Kekere-Ekun

Rahoton NTA ya nuna cewa Shugaba Bola Tinubu ya dawo Najeriya ne a safiyar yau Juma'a.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An ce Tinubu zai rantsar da Mai shari’a Kekere-Ekun a taron majalisar zartarwa na tarayya da zai jagoranta a zauren majalisar da ke Abuja.

A wata sanarwa da Cif Ajuri Ngelale ya fitar a shafinsa na Facebook, ya ce Mai shari’a Kekere-Ekun za ta gaji Olukayode Ariwoola, wanda ya yi ritaya bayan a ranar Alhamis.

Tinubu ya jinjinawa Olukayode Ariwoola

Shugaban kasar ya yabawa Ariwoola bisa nasarar da ya samu a aikin gwamnati da kuma gudunmawar da ya bayar wajen inganta kasar.

“Shugaba Bola Tinubu ya taya Mai shari’a Olukayode Ariwoola murna, yayin da ya yi ritaya a matsayin alkalin alkalan Najeriya bayan kammala aikin gwamnati.
Tinubu ya jinjinawa Ariwoola kan ingantaccen jagoranci na bangaren shari’a da kokarinsa na ganin an tabbatar da kiyaye shari'a kasar."

Kara karanta wannan

Tsohon shugaban INEC ya yi babban rashi da mahaifiyarsa ta rasu a Abuja

- A cewar sanarwar Cif Ngelale.

NJC ta mikawa Tinubu sunan Kekere-Ekun

A makon da ya gabata, muka ruwaito cewa majalisar shari’a ta kasa (NJC) bayan taronta na 106 ta nemi a nada Kudirat Kekere-Ekun a matsayin shugabar alkalai.

Idan Shugaba Tinubu ya rantsar da ita a yau Juma'a, Mai shari'a Kekere-Ekun za ta zama mace ta biyu da ta rike mukamin shugabar alkalai a tarihin kasar.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.