Kasashen Afrika 2 da Najeriya ke Bin Bashin Dala Miliyan 14 na Wutar Lantarki
- Gwamnatin Najeriya ta lissafa kasashe biyu da har yanzu suka gagara biyan kudin wutar lantarkin da aka tura masu a farkon 2024
- Hukumar kula da wutar lantarki ta Najeriya ta bayyana cewa Najeriya na bin kasashen Togo da Benin bashin dala miliyan 14.19
- Rahotanni sun nuna cewa, kamfanoni hudu ne a kasashen biyu da suka ki biyan kudin wutar da suka sha a Janairu, Fabrairu da Maris
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja - Gwamnatin Najeriya na bin kasar Togo da Benin bashin kudin wutar lantarki da suka sha na watanni ukun farkon shekarar 2024 da ya kai dala miliyan 14.19.
Babu daya daga cikin abokan cinikin kasashen waje guda hudu da ya biya kamfanonin samar da wutar lantarki kudin wutar da suka sha na wannan lokaci.
Hukumar kula da wutar lantarki ta Najeriya ta bayyana hakan a wani rahoto da jaridar The Punch ta fitar ranar 22 ga watan Agusta.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Najeriya na bin Togo, Benin bashin wuta
Kamfanonin kasashen wajen su ne Para-SBEE a Benin ($3.15m), Transcorp-SBEE a Benin ($4.46m), Mainstream-NIGELEC a Togo ($1.21m), da Odukpani-CEET a Togo ($5.36m).
NERC ta kara da cewa babu wani yunkuri da abokan huldarta na kasashen waje da ke cikin Najeriya suka yi na biyan N1.86m na kudin wutar da suka sha a farkon shekarar.
Ko da ya ke, hukumar ta bayyana cewa wasu abokan huldarta na kasashen waje (da ke ciki da wajen Najeriya) sun biya bashin da ake binsu na wutar da suka sha a shekarar baya.
"Abokan hulda biyu na kasashe waje sun biya bashin $5.96m. Hakazalika, ofishin gudanar da wutar ya karbi $505.71m daga kwastomominta na kasar waje su takwas."
- A cewar hukumar NERC.
Rashin biyan kudin wuta
Hukumar ta ce tana sa ran kamfanin da ke gudanar da kasuwar wutar zai yi amfani da tanade-tanaden dokokin kasuwar domin dakile abin da ta kira rashin da’a da abokan huldar gida da waje ke nunawa.
A watan Mayu, an ba da rahoton cewa wasu kasashen waje sun gaza tura kusan $51.26m ga Najeriya na kudin wutar lantarki da aka fitar zuwa gare su a shekarar 2023.
Gwamnatin Tarayya ta bayyana hakan a cikin bayanan masana'antar da ke nuna rashin biyan kudaden da abokan huldarta na kasashen waje ke yi, inji rahoton Leadership.
Har ila yau, masu amfani da wutar lantarki na kasashen biyu ba su tura kusan N7.61bn ga bangaren wutar lantarkin Najeriya a shekarar 2023 ba.
An takaita kai wuta waje
A wani labarin, mun ruwaito cewa hukumar NERC ta sanar da takaita samar da wutar lantarki ga abokan huldar dake kasashen Benin, Nijar da Togo.
NERC ta bayyana cewa Najeriya na bin wadannan kasashe bashin Naira biliyan 132.2 na kudin wutar lantarki da aka tura musu daga shekarar 2018 zuwa farkon shekarar 2023.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng