Daga Karbar Kudi Ta Zama Budurwar Wasa a Makaranta, An Ga Gawar Daliba a Bola

Daga Karbar Kudi Ta Zama Budurwar Wasa a Makaranta, An Ga Gawar Daliba a Bola

  • Rundunar 'yan sandan jihar Kwara sun cafke wasu da ake zargi da mutuwar wata dalibar kwalejin kiwon lafiya ta Kwara
  • Kakakin rundunar, DSP Toun Ejire-Adeyemi ta ce an tsinci gawar dalibai mai suna Mojisola Awesu a yashe a kan bola a Ilorin
  • A zantawarmu da Kwamared Zainab Dass, wata shugabar dalibai a jami'ar Abuja, ta koka kan yadda dalibai mata ke yin rayuwar karya

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Kwara - An tsinci gawar wata dalibar kwalejin kiwon lafiya ta Kwara mai suna Mojisola Awesu a kan wata bola a yankin aleniboro da ke Ilorin, babban birnin jihar Kwara.

An ruwaito cewa wata kawar Mojisola ce ta nemi ta zama budurwar wani dalibin wata jami'a kan N15,000 tare da raka shi zuwa wani casu da za a yi.

Kara karanta wannan

A kai zuciya nesa: Matashi ya yi yunkurin aikata sheke-kai bayan bashi ya masa katutu

'Yan sanda sun yi bayanin yadda aka tsinci gawar dalibar kwalejin Kwara
Dalibar Kwaleji ta rasa ranta bayan karbar kwangilar soyayya, 'yan sanda sun magantu. Hoto: @Kwara_PPRO
Asali: Twitter

Kakakin rundunar 'yan sandan Kwara, DSP Toun Ejire-Adeyemi, ta bayyana hakan a wata sanarwa da jaridar The Punch ta samu a ranar Talata.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An tsinci gawar dalibar kwalejin Kwara

A cewar kakakin 'yan sandan, wani mazaunin yankin ne ya kai rahoto a ranar 12 ga Agusta, 2024 cewar wasu leburori sun tsinci gawar dalibar yashe a bola.

DSP Toun ta bayyana cewa 'yan sanda sun garzaya inda abin ya faru tare da dauke gawar wacce aka gano ta dalibar ce mai suna Mojisola, kafin kai ta daki ajiye gawa.

Ta kara da cewa a ranar 13 ga watan Agusta, wata Miss Blessing ta shigar da karar bacewar abokiyar karatunta mai suna Mojisola Awesu, wanda ta fita zuwa wajen casu.

Miss Blessing ta shaidawa 'yan sanda cewa Mojisola ta fita da sabon saurayinta zuwa casun da wasu daliban jami'o'i biyu masu zaman kansu a jihar suka shirya.

Kara karanta wannan

Daga zuwa hawan dutse, dalibi ya fadawa ajalinsa a tafkin kiwon kifi

Daliba ta karbi N15,000 na kwangilar soyayya

Kakakin 'yan sandar ta kara da cewa:

"Miss Mojisola ta samu kiran waya a ranar 9 ga Agusta daga Miss Timileyin, wadda ta sanar da ita casun da daliban jami'ar Summit da Al-Hikmah suka shirya a Ilorin.
"Miss Timileyin ta hada Mojisola da wani dalibi Adebayo Happiness daga jami'ar Summit, wanda suka yi yarjejeniyar biyanta ta N15,000 ta zama budurwarsa domin zuwa casun.
"Da isar ta Ilorin, Miss Mojisola ta sanar da kawarta cewa ta gaza sakin jiki a otal din da Adebayo Happiness ya ajiye ta kuma ta lura cewa babu alamar casu a wajen."

DSP Toun ta kara da cewa bayan gudanar da bincike kan lamarin, an cafke wasu da ake zargi da hannu a lamarin kuma a halin yanzu ana ci gaba da bincike.

Rayuwar karya a manyan makarantu

A zantawarmu da Zainab Abdullahi Dass, mataimakiyar shugabar daliban jami'ar Abuja, ta ce dalibai mata na tafka kuskure a rayuwarsu ta jami'a musamman wadanda suka fito daga gidajen talakawa.

Kara karanta wannan

Ana jimamin kisan sarkin Gobir, 'Yan bindiga sun kashe manoma 13 a Arewacin Najeriya

Kwamared Zainab Dass ta ce sau tari dalibai mata kan dage cewa sai sun yi rayuwa irin da kawayensu masu kudi, musamman mallakar iPone, ko sutura masu tsada.

Shugabar daliban ta ce samari daga ciki ko wajen makaranta kan iya biyawa daliba bukatarta amma da sharadin ita ma sai ta rama biki, inda a karshe da yawa kan yi cikin shege, ko su rasa rayukansu.

Kwamared Zainab Dass ta ce ya kamata abin da ya faru da Mojisola Awesu ya zama darasi ga dalibai mata da ke karatu a manyan makarantu, inda ta ba su shawara a kan su kula da karatunsu.

An tsinci gawar daliba a dakin saurayi

A wani labarin, mun ruwaito cewa an tsinci gawar wata dalibar aji uku a jami'ar Fatakwal (UNIPORT) a dakin saurayinta da ke birnin jihar Ribas.

An ce dalibar mai suna Otuene Justina Nkang ta je dakin saurayin ne kwanaki hudu kafin tsintar gawarta, kuma ana zargin saurayin ya yanke nonuwa da wasu sassan jikinta.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.