An tsinci gawawwakin matasa 17 a gidan casu, Hukumar yan sanda

An tsinci gawawwakin matasa 17 a gidan casu, Hukumar yan sanda

An tsinci gawawwakin matasa akalla goma sha bakwai a gidan casu cikin dare a kudancin kasar Afrika ta kudu, jam’ian hukumar yan sanda sun bayyana.

Kakakin hukumar yan sandan yankin, brigadier Thembinkosi Kinana, ya bayyanawa jaridar AFP cewa dukkan matasan masu matsakaicin shekaru ne na 18 zuwa 20.

Yace:

“Mun samu rahoton cewa kimanin mutum 17 sun mutu a gidan casu dake East London. Har yanzu dai muna gudanar da bincike kan lamarin.”

Afrika ta kudu
An tsinci gawawwakin matasa 17 a gidan casu, Hukumar yan sanda
Asali: UGC

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Yayinda ake yada jita-jitan cewa turereniya ya haddasa kisan wadannan matasa, wani jam’in hukumar kula da lafiya na yankin Eastern Cape, Unathi Binqose, yace karya ne.

Ya bayyanawa AFP cewa:

“Da kamar wuya ace wannan turereniya ne tun da babu wani alamun rauni da aka gani jikin gawawwakin.”

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun sake kai sabon kazamin hari Kaduna, sun kashe jami'an tsaro sun sace dandazon mutane

“Iyayen yaran da basu kwana a gida ba sun taru a wajen don duba gawawwakin domin duba yan uwansu.”

Ya kara da cewa matasan dalibai ne da ke murnar kammala jarabawarsu na sakandare.

Asali: Legit.ng

Online view pixel