Gwamna Ya Sanar da Sabon Tsarin Albashi ga Ma’aikatan Jiharsa? Gaskiya Ta Fito

Gwamna Ya Sanar da Sabon Tsarin Albashi ga Ma’aikatan Jiharsa? Gaskiya Ta Fito

  • Gwamnatin Kebbi ta yi karin haske kan wata takarda da take yawo a soshiyal midiya wadda ta nuna sabon tsarin albashin ma'aikatan jihar
  • Shugaban ma’aikatan Kebbi, Safiyanu Garba-Bena ya bayyana cewa wannan takarda ba daga gwamnatin jihar ta fito ba, karya aka shirya
  • Alhaji Safiyanu ya yi kira ga ma'aikatan jihar Kebbi da su kara hakuri tare da jinkirtawa zuwa lokacin da tsarin albashin zai fito a hukumance

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Kebbi - Gwamnatin Kebbi ta yi magana kan rahotannin da ake yadawa a soshiyal midiya cewa ta fitar da sabon tsarin albashi da alawus ga ma'aikatan jihar.

Wata takarda mai taken 'Tsarin albashi da alawus na ma'aikatan jihar Kebbi 2024' da ta yadu a soshiyal midiya ta nuna cewa gwamnatin jihar ta fitar da sabon albashin ma'aikata.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun saki bidiyon Sarkin da suka sace, wa'adin kai kudi ya kare

Gwamnatin Kebbi ta yi magana kan sabon tsarin albashin ma'aikata
Gwamnatin Kebbi ta nesanta daga sabon tsarin albashin jihar da ke yawo. Hoto: @KBStGovt
Asali: Facebook

Karyata wannan rahoto na kunshe a cikin wata sanarwa daga shugaban ma’aikatan Kebbi, Alhaji Safiyanu Garba-Bena da aka wallafa a shafin gwamnatin jihar na Twitter.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Alhaji Safiyanu Garba-Bena, ya kara da cewa:

“Muna kira ga ma’aikatan gwamnati da sauran jama’a da su yi watsi da wannan takarda, su kuma yi hakuri su jira tsarin albashi na gwamnati a hukumance.

Garba-Bena ya nuna jin dadin gwamnatin jihar bisa hakuri, fahimta da juriyar ma’aikatan Kebbi da kungiyoyin kwadagonsu inda ya nemi su ci gaba da hakan.

Ya kuma tunatar da ma’aikatan yadda gwamnansu ke da alaka mai karfi da kungiyar kwadago, inda ya ce:

“Mai kaunarku, mai girma Gwamna Nasir Idris, ya taba zama dan kungiyar kwadago kuma ya dukufa ainun wajen kyautata rayuwar ma’aikata.
Gwamnati na aiki tukuru domin tabbatar da jin dadi da gamsuwar dukkanin ma’aikatan jihar. Kauran ya kasance mai son 'yan kwadago kuma ba zai kyale ma'aikata su tagayyara ba."

Kara karanta wannan

An zargi Gwamnatin shugaba Tinubu da satar dabarar tattalin arziki a wajen Atiku

- A cewar sanarwar Garba-Bena.

Duba sanarwar a kasa:

Gwamna ya dauki matsaya kan sabon albashi

A wani labarin, mun ruwaito cewa Gwamnan jihar Kebbi, Nasir Idris ya ce a shirye ya ke ya biya dukkanin sabon mafi karancin albashi da aka amince da shi.

Gwamnan ya bayyana haka ne a yau Laraba 19 ga watan Yuni inda ya barranata kansa da wasu gwamnoni da suka ce ba za su iya biyan sabon albashin ba.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.