Gwamnatin Kebbi za ta soma biyan sabon mafi karancin albashi a watan Satumba – SSG
Gwamnatin jihar Kebbi ta ce za ta fara biyan ma’aikatanta sabon mafi karancin albashin naira 30,000 daga karshen watan Satumba.
Sakataren gwamnatin jihar Kebbi, Alhaji Babale Yauri ne ya fitar da wannan sanarwa ranar Litinin 23 ga watan Satumba a Birnin Kebbi babban birnin jihar Kebbi.
KU KARANTA:Gwamna Badaru ya nada mashawarta na musamman guda 15 a Jigawa
“Kaddamar da wannan mafi karancin albashin na zuwa daidai da rattaba hannun Shugaba Buhari game da mafi karancin albashin, domin karfafawa ma’aikatan Kebbi gwiwa.
“Gwamna Bagudu ya bada umarnin a soma biyan ma’aikatan Kebbi naira 30,000 daga karshen watan Satumba, 2019.” Inji Babale.
Ya kara da cewa, gwamnati ta aminta da kaddamar da mafi karancin albashin ne a dalilin tattaunawa da Majalisar dokokin jihar Kebbi, shuwagabannin kungiyar ‘yan kwadago da kuma sauran hukumomin gwamnati.
“Duk da karancin kudi da gwamnatinmu ke fama da shi, Gwamna Atiku Bagudu ya aminta da fara biyan wannan mafi karancin albashin na naira 30,000.
“Babu wani ma’aikacin gwamnatin jihar da zai rika karbar kasa da N30,000. Kananan hukumomi muna umurtarsu da su yi gyara domin soma biyan mafi karancin albashin.” Inji Babale.
A wani labari mai kama da wannan za ku ji cewa, Gwamnan jihar Jigawa, Muhammad Badaru Abubakar ya nada sabbin mashawartan gwamnatinsa guda 15.
Idan baku manta ba dai, har ila yau Gwamna Badaru bai nada majalisar zartarwa ba, a don haka wannan shi ne nadi mafi girma da yayi tun bayan rantsar da shi a wa’adinsa na biyu, daga watan Mayu, 2019 zuwa yanzu.
https://tribuneonlineng.com/kebbi-commences-new-minimum-wage-payment-september-%e2%80%95-ssg/
Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa
ko a http://twitter.com/legitcomhausa
KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com
Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa
Asali: Legit.ng