'Yan Bindiga Sun Kai Farmaki, Sun Yi Garkuwa da Daliban Kwalejin Kiwon Lafiya

'Yan Bindiga Sun Kai Farmaki, Sun Yi Garkuwa da Daliban Kwalejin Kiwon Lafiya

  • Wasu ‘yan bindiga sun yi garkuwa da dalibai biyar a kwalejin fasahar kiwon lafiya ta jihar Enugu da ke karamar hukumar Oji
  • An ce 'yan bindigar sun kai harin ne a daidai lokacin da daliban ke fitowa daga harabar makarantar a yammacin Alhamis
  • Da yake tabbatar da kai harin, kakakin ‘yan sandan Enugu, DSP Daniel Ndukwe a ranar Lahadi ya ce yanzu an kubutar da dalibai 2

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Enugu - Wasu mahara dauke da makamai sun yi garkuwa da dalibai 5 na kwalejin fasahar kiwon lafiya ta jihar Enugu da ke karamar hukumar Oji.

An tattaro cewa lamarin ya faru ne a lokacin da daliban ke barin harabar makarantar.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga: Ana cikin tashin hankali a Sokoto, wa'adin karbo Sarkin Gobir ya kare

'Yan bindiga sun sace daliban kwalejin kiwon lafiya a Enugu
'Yan sanda sun tabbatar da sace dalibai 5 na kwalejin kiwon lafiya da ke Enugu. Hoto: Legit.ng
Asali: Original

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa an ga wani mutum cikin jini a wani faifan bidiyo da ke yawo a shafukan sada zumunta a ranar Asabar jim kadan bayan harin da aka kai.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

'Yan bindiga sun sace daliban kwaleji

Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar Enugu, DSP Daniel Ndukwe, ya tabbatar da faruwar lamarin a wata sanarwa da ya fitar ranar Lahadi.

DSP Daniel Ndukwe ya bayyana cewa 'yan bindigar sun kai harin ne da yammacin ranar Alhamis.

Ya fayyace cewa rahotannin da ke nuni da cewa an sace “dalibai marasa adadi” ba hakan ba ne, an zuzuta adadin mutanen ne kawai.

Matakin da 'yan sanda suka dauka

DSP Ndukwe ya bayyana cewa ‘yan sanda sun samu rahoton harin kuma cikin gaggawa suka mayar da martani, inda suka yi nasarar ceto biyu daga cikin daliban da aka sace.

Kara karanta wannan

Zaben 2027: Fastocin takarar shugaban kasa na Ganduje sun mamaye soshiyal midiya

Sai dai kakakin 'yan sandan ya ce akwai wasu dalibai uku da har yanzu ba a gansu ba, inji rahoton jaridar Independent.

Ya kuma bayar da tabbacin cewa an kaddamar da wani gagarumin yunkurin ceto sauran daliban da aka kama tare da damke masu garkuwa da mutanen.

'Yan bindiga sun sace shugaban kwaleji

A wani labarin, mun ruwaito cewa wasu 'yan bindiga sun yi garkuwa da shugaban kwalejin fasaha ta jihar Benue, Dakta Emmanuel Barki.

An ce 'yan bindigar sun sace Dakta Emmanuel da wasu ma'aikatan kwalejin a kan hanyar su ta dawowa zuwa Ugbokolo bayan sun je wani aiki a Makurdi.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.