An Yi Rashi: Shugaban Jam'iyyar APC Ya Riga Mu Gidan Gaskiya
- Jam'iyyar APC mai adawa a Oyo ta yi babban rashi bayan shugabanta na jihar ya riga mu gidan gaskiya
- Marigayi Barista Isaac Ajiboye Omodewu, ya rasu ne yana da shekara 61 a duniya da safiyar ranar Litinin
- Isaac Ajiboye kafin rasuwarsa ya taɓa riƙe muƙamin kwamishina har sau biyu a gwamnatin tAjiboa Ajimobi
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Oyo - Shugaban jam’iyyar APC reshen jihar Oyo, Barista Isaac Ajiboye Omodewu, ya riga mu gidan gaskiya yana da shekara 61.
Isaac Ajiboye Omodewu wanda haifaffen ƙaramar hukumar Itesiwaju ne ya rasu ne a safiyar ranar Litinin, 19 ga watan Agustan 2024.
Shugaban APC na Oyo ya rasu
Shugaban na babbar jam’iyyar adawa a jihar, ya rasu ne kimanin shekara guda bayan ya kammala jinyar wata cuta da ba a bayyana ba.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wani jigon jam'iyyar APC, Akin Akinwale, a jihar ya tabbatar da rasuwarsa a shafinsa na X.
Sakataren yaɗa labarai na jam’iyyar APC a jihar Oyo, Olawale Sadare ya tabbatar da rasuwar shugaban jam’iyyar.
Wane ne Isaac Ajiboye Omodewu?
Isaac Ajiboye ya riƙe muƙamin kwamishinan ƙananan hukumomi da harkokin masarautu, kwamishinan filaye da gidaje a gwamnatin marigayi tsohon Gwamna Abiola Ajimobi.
Marigayin shugaban na APC yana da katin shaidar zama ɗan ƙasar Amurka.
Jaridar Leeadership ta ce kwanan nan ya kammala karatunsa na digirin digirgir a fannin lauya.
Karanta wasu labaran kan rashe-rashe
- Bayan rikici kan naɗinsa, basarake ya rasu watanni kadan da karbar sarauta
- Kwamishinan Bauchi ya rasu yana da shekara 60 a duniya
- Babban basarake ya rasu jim kaɗan bayan dawowa daga Sallar Idi
Kawun Pantami ya riga mu gidan gaskiya
A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon ministan Najeriya kan tattalin arziki na zamani, Farfesa Isa Ali Pantami ya sanar da rasuwar yayan mahaifiyarsa.
Farfesa Isa Pantami wanda ya yi minista a zamanin mulkin Buhari ya ce kawun nasa, Malam Abubakar Audu ya rasu yana da shekaru masu yawa a duniya.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng