Magungunan Gargajiya masu maganin cutar Amai da Gudawa, wato Kwalara

Magungunan Gargajiya masu maganin cutar Amai da Gudawa, wato Kwalara

- Yanzu lokaci ne na damina a yankunan arewa, ana kuma samun barkewar cutar Cholera

- Halin mu na kazanta, da yin bayan gida a waje, wanda ruwa ke wanke wa zuwa gonaki da guraben ruwan sha. Kudaje ma kan yada wannan cuta ta zamo annoba.

- Kowanne ilimi na gargajiya dai yana bayan na kimiyya, wanda farko shine tsafta, kiyayewa da kuma ilminin sanin yadda ake hada ruwan gishiri da siga.

Cutar amai da gudawa da aka fi sani da kwalera ta bulla a sassan Najeriya, abin da masana suka ce ba zai rasa alaka da annobar ambaliyar ruwa da yanayin kazantar muhalli ba.

Magungunan Gargajiya masu maganin cutar Amai da Gudawa, wato Kwalara
Magungunan Gargajiya masu maganin cutar Amai da Gudawa, wato Kwalara

Hukumar kula da lafiya ta duniya ta bayyana cewa ana kamuwa da cutar amai da gudawa ne ta hanyar ci ko shan gurbataccen abinci ko ruwa sannan kuma cutar bata nuna wasu alamu kafin barkewarta, kuma tana iya kisa matukar ba a magance ta ba. Saidai abin da mutane da yawa basu sani ba shine ana iya magance cutar amai da gudawa a gida ta hanyar amfani da sahihan magungunan gargajiya. Ga wasu daga cikin su.

1. Kunun masara, ganyen shuwaka da na goba.

Wata jaridar kimiyyar lafiya ta Afirka ce ta tabbatar da tasirin hadin kunun masara da ganyen shuwaka da na goba wajen magance amai da gudawa.

2. Bakar Tsamiya

Bincike ya nuna cewar bayan amfanin bakar tsamiya wajen magance cututtuka da dama da suka hada da tari, shawara, da basur, ana iya amfani da ita domin magance amai da gudawa. Wasu malaman kimiyya ne a wata jami'a da ke Afirka ta kudu, "university of fort hare", suka gudanar tare da wallafa hakan.

DUBA WANNAN: Sanata Kwanwaso ya karyata komawarsa PDP

3. Tabo

Duk da kasancewar abin kamar maras yiwuwa, ana amfani da tabo domin tsayar da amai, hana barin ciki ga mata masu juna biyu, tsayar da gudawa, da magance cututtukan fata.

Wani masanin tsirrai kuma mai bincike a sashen hadin Magani, mista Isaac T. Adeleke, a jami'ar Lagos da ke Idi - Araba ya tabbatar da haka.

4. Gawayi

A kauyaukan Najeriya an dade ana amfani da gawayi wajen wanke hakora, kashe tasirin guba, da kuma adana wake. Yanzu haka masana kimiyya sun kara gano cewa ana iya amfani da gawayi domin magance amai da gudawa.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng