Janye Dakarun Soji: 'Yan Bindiga Sun Kwace Gidajen Mutane, Sun Fara Noma a Arewa

Janye Dakarun Soji: 'Yan Bindiga Sun Kwace Gidajen Mutane, Sun Fara Noma a Arewa

  • Mazauna kauyen Allawa da ke karamar hukumar Shiroro, jihar Neja sun yi wani yunkuri na komawa muhallansu bayan wata biyar
  • Sai dai wasu da aka tura domin duba halin da garin ke ciki, sun ce 'yan bindiga sun kwace gidajen da kuma yin shuka a gonakinsu
  • A watan Afrilu ne mazauna Allawa suka yi gudun hijira saboda tsoron hare-hare bayan da aka janyen dakarun soji da ke tsaron yankin

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Neja - Akalla wata biyar ke nan da al'ummar garin Allawa da ke karamar hukumar Shiroro, jihar Neja suka yi kaura daga gidajensu bayan janye sojojin da ke tsaron yankin.

An ruwaito cewa bayan tafiyar sojojin, mazauna Allawa sun firgita, wanda ya sa suka gudu yayin da 'yan bindiga suka kwace gidajensu tare da fara yin noma a garin.

Kara karanta wannan

Jigawa: Wasu matasa 2 sun mutu a yanayi mai ban tausayi a hanyar zuwa Kasuwa

'Yan bindiga sun kwace gidaje da gonakin 'yan gudun hijira a jihar Neja
'Yan bindiga sun koma yin Noma bayan tilasta mazauna kauyen Neja yin gudun hijira.
Asali: Original

Mutanen Allawa sun yi shirin komawa gida

Daya daga cikin 'yan gudun hijirar a Erena ya shaidawa Daily Trust cewa an tura wasu mutane zuwa Allawa domin dubawa ko za su 'yan garin za su iya komawa gidajensu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sai dai mutanen sun dawo da labari marar dadi, inda suka shaida cewa 'yan bindigar sun gaje gidajensu, kuma sun yi shuka a gonakinsu, don haka maganar komawa babu ita.

Ya ce ‘yan ta’addan sun kuma yi amfani da takin da suka saya kafin su gudu daga gidajensu kan amfanin gonakinsu, inda kuma suka lalata da kona wasu gidaje.

Alklawa: 'Yan bindiga sun gaje gidaje da gonaki

Dan gudun hijirar ya ce:

“Mun je ne domin duba gidajenmu domin sanin ko al’ummarmu za su iya komawa muhallansu, amma abin mamaki a yanzu ‘yan ta’addan sun gaje garin Allawa.

Kara karanta wannan

Gwamna ya fada hannun ƴan damfara, ana tura sakon neman kudi a lambarsa ta WhatsApp

"Mun ga su; sun noma mafi yawan filayen noman mu. Sun yi amfani da takin da muka sayo domin yin noma da shi kafin a raba mu da muhallanmu a watan Afrilu.
“Sun lalata wasu gidajen mu, sun kuma gaje sauran. Gidanmu na daga cikin wadanda suka lalata. Abin daga hankali ne."

An janye sojoji daga yankin Allawa

Tun da fari, mun ruwaito cewa mutane sun shiga fargaba bayan sojoji sun tashi daga sansaninsu da ke kauyen Allawa a karamar hukumar shiroro a jihar Neja.

An ce tashin sojojin ya tilasta mazauna yankin tsallake gidajensu inda suka yi tafiyar kilomita 50 domin neman tsira saboda tsoron hare-haren 'yan bindiga.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.