'Yan Bindiga Sun Saki Bidiyon Sarkin da Suka Sace, Wa'adin Kai Kudi ya Kare
- 'Yan bindiga sun saki bidiyon Sarkin Gobir, Hakimin Gatawa, Alhaji Isa Muhammad wanda suka yi garkuwa da shi a watan Yuli
- A cikin bidiyon wanda aka ga sarkin daure cikin sarka ya roki gwamnatin Sokoto da ta kai masa dauki ta hanyar biyan kudin fansa
- Sarkin Gobir wanda aka ga rigarsa ta jike da jini ya ce 'yan bindigar sun gaji da jiran kai kudin, kuma za su halaka shi idan suka ji shiru
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Sokoto - Har yanzu Sarkin Gobir kuma Hakimin Gatawa da ke karamar hukumar Sabon birni a jihar Sokoto, Isa Muhammad Bawa na hannun 'yan bindiga.
A wani faifan bidiyo da 'yan bindigar da suka sace basaraken suka saki, Alhaji Isa ya roki gwamnatin Sokoto ta taimaka ta biya kudin fansarsa.
A cikin bidiyon, wanda wani Hamza Suleiman ya wallafa a shafinsa na X, Sarkin Gobir ya shaidawa gwamnati cewa 'yan bindigar sun ba da wa'adin kai kudin.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Dan majalisa ya gaskata bidiyon sarki
Sarkin wanda aka yi garkuwa da shi kwanaki kusan 22 da suka gabata, an gan rigarsa ta jike da jini yayin da aka daure hannayensa da kafafunsa da sarka.
Legit Hausa ba ta iya tantance faifan bidiyon da kanta ba, amma dan majalisar da ke wakiltar Sabon Birni a majalisar dokokin jihar, Aminu Boza ya tabbatar da cewa wanda ke cikin bidiyon shi ne Hakimin.
Hon. Aminu Boza ya tabbatar da hakan ne a wani rahoto da jaridar Daily Trust ta fitar a ranar Asabar, 17 ga watan Agusta.
Sarkin Gobir ya nemi daukin gwamnati
A cikin faifan bidiyon, Sarkin Gobir, Isa Muhammad ya nemi daukin gwamnatin Sokoto yana mai cewa:
"Ina sanar da 'yan uwana, masu fatan alheri, abokai da shugabanni cewa yau (Laraba) ita ce ranar karshe, don haka idan suna son su taimake ni, to su yi hakan yanzu.
“Na rantse da Allah madaukakin sarki cewa ko su (’yan bindigan) sun gaji saboda su ma sun yi iya kokarinsu amma babu wani yunkuri daga gwamnati.
"Ina fatan samun taimakon su (gwamnati) saboda na yi musu hidima kusan shekaru 45, a bangaren sarautar gargajiya."
Idan har an dauki bidiyon ranar Larabar da ta gabata ne, to zuwa yanzu wa'adin da 'yan bindigar suka diba na kai kudin ya kare.
Sai dai har yanzu ba a sake jin wani labari game da halin da basaraken da dansa da aka sace su tare suke ciki ba.
Kalli bidiyon a kasa:
'Yan bindiga sun sace Sarkin Gobir
Tun da fari, mun ruwaito cewa 'yan bindiga sun kai hari tare da yin awon gaba da Sarkin Gobir na yankin Gatawa, Isa Bawa tare da dan cikinsa a titin Sokoto zuwa Sabon Birni.
Kakakin rundunar ’y an sandan jihar Sokoto, Ahmed Rufa’i, ya tabbatar da faruwar yin garkuwa da basaraken bayan 'yan bindiga sun budewa motar da yake ciki wuta.
Asali: Legit.ng