Bayan Caccakar Tinubu: Obasanjo Ya Fadi abin da ke Kawo Cikas ga Ci Gaban Najeriya

Bayan Caccakar Tinubu: Obasanjo Ya Fadi abin da ke Kawo Cikas ga Ci Gaban Najeriya

  • Olesugun Obasanjo ya ce babbar matsalar da ke hana Najeriya ci gaba ita ce shugabanci, yana mai alakanta hakan da gurbatattun shugabanni
  • A cewar tsohon shugaban kasar, idan har aka samu shugabanni na gari a dukkanin matakan gwamnati, to za a samu ci gaba a kasar nan
  • Obasanjo wanda ya ce shugabanni marasa ilimi, masu karancin tunani ke mulkar kasar nan, ya nemi 'yan Najeriya su yi karatun ta-nutsu

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Ogun - Tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo ya ce shugabanci ne matsalar Najeriya, yana mai cewa idan kasar ta samu shugabannin na-gari, komai zai daidaita.

Olusegun Obasanjo ya ce shugabanni masu tsukakken tunani a dukkanin matakan gwamnati ne ke jawo koma baya ga ci gaban kasar.

Kara karanta wannan

"Kasar mu ce duka," Cif Obasanjo ya yi barkwanci kan zargin asalinsa Ibo ne

Olusegun Obasanjo ya yi magana kan matsalar Najeriya
Obasanjo ya ce shugabanci ne matsalar Najeriya. Hoto: @Oolusegun_obj
Asali: Getty Images

Tsohon shugaban kasar ya yi kira ga 'yan Najeriya da su rika zabar shugabanni nagari, masu sanin ya kamata idan har suna so kasar ta ci gaba, inji rahoton Channels TV.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Matsalar da Najeriya ke fama da ita

Dattijon ya yi magana ne a Abeokuta, babban birnin jihar Ogun a taron 2024 na cibiyar bunkasa shugabanci ta kasa-da-kasa (LEIC).

Obasanjo ya ce:

" Domin Nijeriya ta samu ci gaba daga halin da take ciki a yanzu, dole ne ayi waje da shugabanni masu tsukakken tunani daga kowane mataki na mulki."

Ya ce a halin yanzu kasar nan a dukkanin matakan gwamnati na fama da matsaloli ta dalilin wasu gungun shugabanni masu karancin ilimi, son kai da rashin iya gudanar da mulki.

Obasanjo ya ba 'yan Najeriya shawara

Jaridar This Day ta ruwaito Obasanjo ya kalubalanci ’yan Najeriya da su kawo karshen dabi'ar dora shugabanni marasa lissafi kan mulki tare da zabar wadanda za su yi masu aiki kawai.

Kara karanta wannan

Gwamna ya jingine Atiku, ya faɗi mutum 1 da ya kamata ya karɓi mulkin Najeriya a 2027

“Kuma idan ka tambaye ni a kalma daya, mecece matsalar Nijeriya a yau? Ba zan yi dogon tunani ba, zan ce shugabanci ne.
"Shugabancin da aka takaita shi kan abu daya, shugabancin da babu ilimi da sanin mulki a ciki, shugabancin da babu tunanin ci gaban al'umma a cikinsa.
"Idan har za mu iya zabar shugabanni na gari, to komai zai daidaita. Dole mu rika tunatar da jama'a su zabi shugabanni na gari a dukkanin matakai."

Obasanjo ya fallasa gwamnatin Tinubu

A wani labarin, mun ruwaito cewa Olusegun Obasanjo ya ce gwamnatin Bola Tinubu ta dawo da biyan tallafin man fetur sabanin abin da shugaban kasar ya ce a jawabinsa na kai tsaye.

Olusegun Obasanjo ya ce Shugaba Tinubu ya dawo da biyan tallafin fetur din ne sakamakon hauhawar farashin kayayyaki da kasar ke fuskanta.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.