Buga Takardun Naira: EFCC Ta Gano Yadda Tsohon Gwamnan CBN Ya Barnatar da N19bn
- Tsohon gwamnan CBN, Godwin Emefiele ya sake shiga wata sabuwar matsala yayin da aka bankado wata badakar N18bn a 2014
- Wani bincike da aka ce hukumar EFCC ta gudanar ya nuna cewa Emefiele ya yi amfani da N18bn wajen buga N1bn da sayen kayan sitamfi
- Binciken ya kuma gano cewa tsohon gwamnan CBN ya nemi izinin tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan kafin ya fitar da kudin
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja - Ana zargin cewa sabon binciken da hukumar EFCC ta gudanar ya bankado yadda tsohon gwamnan CBN, Godwin Emefiele ya kashe N19bn wajen buga takardun Naira.
Binciken ya nuna cewa Emefiele ya barnatar da N19bn wajen buga Naira biliyan 1 a takardar N100 da kuma sayo kayayyakin buga sitamfi na alfarma guda 5,000.
Kamar yadda jaridar Leadership ta ruwaito, tsohon gwamnan na CBN ya yi amfani da wani babban biki da Najeriya za ta yi a 2014 wajen barnatar da kudin.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Jonathan ya ba Emefiele izinin cire kudin
Wata majiya daga hukumar EFCC ta bayyana cewa Emefiele ya rubuta takarda zuwa ga tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan a ranar 1 ga Satumbar 2014 kan taron.
A cikin takardar, tsohon gwamnan ya bukaci Jonathan ya amince ya buga takardun kudin da sayo kayan sitamfin ba tare da an tuntubi mahukuntan CBN ba, sabanin dokar CBN ta 2007.
An ce tsohon shugaban kasar ya amincewa Emefiele ya buga takardun kudin kafin neman sahalewar mahukuntan CBN, wanda ya saba da sashe na 19(1)(b) na dokar CBN, 2007.
CBN ya ba kamfanin Sweden kwangilar kudin
An ba da kwangilar buga takardun N100 har na Naira biliyan 1 da kuma samar da kayayyakin buga sitamfi guda 5000 a kan N18,911,524,842.62.
An ce an ba kwangilar ne ga wani kamfanin Sweden mai suna Crane Currency, Sweden (kamfanin da ya saba yiwa CBN aikin buga takardun kudi da makamantansu).
A 17 ga Satumbar 2014 ne aka ce Emefiele ya ba kamfanin Crane Currency kwangilar. An fara biyan kafin alkalami na dala miliyan 73, wanda ya kai kusan kaso 60 na gaba daya kudin kwangilar.
Yadda Emefiele ya barnatar da N19bn
Kamfanin ya samu wannan kudin ne ta hanyar sashen ayyuka na kudi na CBN, wanda hakan ya sabawa tsarin da aka kafa na biyan manyan kwangilolin kudi ta hanyar takardar bashi.
Ko da yake an ce dala 72,996,00.00 ne aka turawa Crane Currency, amma an gano cewa dala 39,848,991.90 ne kadai ya shiga asususn kamfanin.
Binciken ya nuna cewa an Emefiele ya ki tura sauran dala 32,716,050.00 wanda aka sauya zuwa Naira a farashin canji na kowace dala 1 a kan Naira 162.
An ce an raba Naira Biliyan 5.3 ga wasu mutane da da suke da hannu a kwangilar. Amma binciken jaridar ya nuna cewa zuwa yanzu EFCC ta kwato Naira biliyan 3.2 daga mazambatan.
Kakakin hukumar EFCC ya yi magana
Da aka tuntubi mai magana da yawun hukumar ta EFCC, Dele Oyewale, ya tabbatar da cewa hukumarsa na gudanar da bincike kan lamarin amma ya ki bayar da karin bayani.
"Babu wani abu da zan iya fada muku a halin yanzu saboda har yanzu jami'anmu na bincike kan lamarin," in ji Mista Oyewale.
Rahoton ya ce an kasa samun Mista Emefiele don jin ta bakinsa. Duka layukan wayar da aka kira ba sa tafiya.
Kotu ta kwace kudi da kadarorin Emefiele
A wani labarin, mun ruwaito cewa wata babbar kotun tarayya da ke Legas ta ba da umarnin a kwace $2,04m da aka alakanta su da Godwin Emefiele, tsohon gwamnan CBN.
Hakazalika, kotun ta ce a kwace wasu kadarori 7 da hannayen jari biyu da tsohon gwamnan bayan EFCC ta yi zargin cewa an same su ta haramtacciyar hanya.
Asali: Legit.ng