Da gaske mun buga kudi, amma rance muka baiwa gwamnoni: Gwamnan CBN

Da gaske mun buga kudi, amma rance muka baiwa gwamnoni: Gwamnan CBN

- Gwamna Godwin Emefiele ya fayyace gaskiya kan lamarin buga kudi

- Gwamnan Edo da Ministar kudi na musayar kalamai kan lamarin

- Wannan ya biyo bayan ikirarin Gwamna Obaseki na cewa Najeriya na cikin hali mai wuya

Gwamnan babban bankin Najeriya CBN, Godwin Emefiele, ya yi fashin baki kan musayar kalaman dake faruwa tsakanin gwamnan jihar Edo, Godwin Obaseki, da Ministar Kudi, Zainab Ahmed.

A makon jiya, mun kawo muku cewa Gwamnan jihar Edo, Godwin Obaseki, ya bayyana cewa Najeriya na cikin halin rashin kudi saboda sai da aka buga wasu biliyoyi a watan Maris aka rabawa jihohi.

Amma a ranar Laraba Gwamnatin tarayya ta siffanta kalaman gwamnan jihar Edo, Godwin Obaseki, na cewa an buga kudi N60bn don rabawa gwamnoni a matsayin karya maras tushe da asali.

Ministar kudi da kasafi, Zainab Ahmed Shamsuna, ta bayyana hakan yayin hira da manema labaran fadar shugaban kasa ranar Laraba.

Martani kan hakan, ranar Alhamis Gwamnan jihar Edo, Godwin Obaseki ya bayyana cewa ba zai yi cacan baki da gwamnatin tarayya kan maganar da yayi na cewa an buga N60bn a Maris don rabawa gwamnoni.

Raba gardama kan wannan lamari, gwamnan CBN, Godwin Emefiele ya bayyana cewa abinda Obaseki ke nufi da buga kudi shine kudin da aka baiwa gwamnoni rance.

Ya ce ba zai yiwu gwamnatin tarayya ta zuba ido al'ummar Najeriya su shiga garari don rashin kudi ba.

Yace: "Maganar buga kudi kawai rance muka bada kuma wannan aikinmu ne... Ba zai yiwu CBN ko wani bankin kasa ya zuba ido ya ki taimakon gwamnati a irin wannan lokaci ba."

KU KARANTA: Jerin jihohi 5 da suka fi aiwatarwa al'ummarsu manyan ayyuka na kasafin kudi, Kaduna ce ta farko

Da gaske mun buga kudi, amma rance muka baiwa gwamnoni: Gwamnan CBN
Da gaske mun buga kudi, amma rance muka baiwa gwamnoni: Gwamnan CBN
Asali: UGC

A bangare guda, Dirakta Janar na Ofishin manajin basussukan Najeriya DMO, Patience Oniha, ta ce basussukan da ake bin gwamnatin tarayya da gwamnatocin jihohin yanzu ya kai N33.63 trillion.

A jawaban da ta saki a shafin sadarwanta na Tuwita, Oniha ta ce jita-jitan da ake yadawa kan adadin bashin da ake bin Najeriya yasa ta wallafa jerin basussuka.

A cewarta, "yana da muhimmanci in fayyace cewa wannan bashin na gwamnatin tarayya ne, birnin tarayya, da jihohin Najeriya 36,"

Asali: Legit.ng

Online view pixel