Hankula Sun Tashi, Yan Bindiga Sun Sace Dalibai Likitoci daga Jami’o’in Arewa

Hankula Sun Tashi, Yan Bindiga Sun Sace Dalibai Likitoci daga Jami’o’in Arewa

  • Rahotanni na nuni da cewa yan bindiga sun sace wasu ɗalibai da suke kan hanya daga Arewa zuwa Kudu domin halartar taro
  • Bayanai sun nuna cewa ɗaliban masu karatun likita wanda sun kai akalla 20 sun fito ne daga jami'o'in Maiduguri da jihar Filato
  • Kakakin rundunar yan sandan Benue ta yi karin haske kan halin da ake ciki kasancewar an sace daliban ne bayan shiga cikin jihar

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Benue - An sace dalibai masu karatun likita da suka fito daga jihohin Arewa zuwa Kudu domin halartar wani taro.

Rahotanni sun nuna cewa ɗaliban sun fito ne daga jihohin Borno da Filato za su wuce jihar Enugu a Arewacin Najeriya.

Kara karanta wannan

Tinubu ya fito da salon tsarin tsaro a Arewa domin maganin yan bindiga

Benue
An sace dalibai 20 a Benue. Hoto: Legit
Asali: Original

Jaridar Leadership ta wallafa cewa rundunar yan sandan jihar Benue ta tabbatar da faruwar lamarin.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An sace dalibai likitoci 20 a Arewa

Bayanai da suka fito daga jihar Benue sun nuna cewa an sace dalibai masu karatun likita har su 20.

Rahoton the Cable ya nuna cewa an sace daliban ne da misalin karfe 5:30 na yamma a karamar hukumar Otukpo ta jihar Benue.

Daga ina daliban likitocin suka fito?

Bincike ya nuna cewa an sace daliban ne yayin da suka fito daga jami'o'in Maiduguri da Filato za su tafi jihar Enugu.

Daliban za su halarci taron kungiyar likitocin cocin Katolika ne yayin da aka kama su a yammacin ranar Alhamis.

Sace dalibai: Maganar yan sandan Benue

Kakakin rundunar yan sandan jihar Benue, Catherine Anene ta tabbatar da faruwar lamarin ta wayar tarho.

Kara karanta wannan

Jigawa: Wasu matasa 2 sun mutu a yanayi mai ban tausayi a hanyar zuwa Kasuwa

Sai dai Catherine Anene ta ce ba su samu tabbas a kan adadin daliban ba kuma a halin yanzu suna bincike kan lamarin.

An kubutar da dalibai a Kogi

A wani rahoton, kun ji cewa kwanaki da yin garkuwa da daliban jami'ar kimiyya da fasaha ta Confluence (CUSTECH) da ke Osara an fita neman su.

Rundunar 'yan sandan jihar Kogi, ta ce jami'an tsaro, ciki har da mafarauta, sun yi nasarar kubutar da wasu daga cikin daliban.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng