Dan Najeriya Ya Fadi Matakan da Ya bi Wajen Samun Tallafin Karatu Kyauta a Ingila

Dan Najeriya Ya Fadi Matakan da Ya bi Wajen Samun Tallafin Karatu Kyauta a Ingila

Tunanin fita kasar waje domin neman ilimi na iya zama abin sha'awa ga dalibai. Sai dai, tunanin irin makudan kudin da ake kashewa na iya kashe guiwar dalibi.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Duk da haka, bai kamata dalibi ya bari matsalar kudi ta ruguza burinsa ba; samun tallafin karatu na ba da dama ga dalibi ya yi karatu mai inganci, ba tare da ya biya sisin kwabo ba.

Kusan tallafin karatu guda biyu ne: Wanda ake daukewa dalibi dukkanin dawainiyar karatu, da kuma wanda ake biya masa wani kaso na kudin da zai kashe a karatun.

Dan Arewa ya yi bayanin yadda daliban Najeriya za su iya samun tallafin karatu a waje
Bayanin yadda ake neman tallafin karatu a kasashen waje daga Dakta Attahiru Dan-Ali. Hoto: LumiNola
Asali: Getty Images

Idan kuna neman ƙarin bayani game da nau'ukan tallafin karatu, dabarun neman tallafin, takardun da ake bukata da shawarwari, to ku ci gaba da karanta wannan rubutu.

Kara karanta wannan

Tsarin Tinubu ya jefa jami'o'i a matsala, za a ƙarawa dalibai N80,000 a kudin makaranta

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Nau'ukan tallafin karatu a kasashen waje

Akwai nau'ukan tallafin karatu da dama, amma muhimman su ne shirin tallafi na FFSP wanda kasar Amurka ke bayarwa ga daliban da ke son yin karatu a kasarta.

A Faransa kuwa, manyan makarantu na ba da dama ga daliban kasashe su yi karatu kyauta karkashin shirinsu na EESP, amma ga daliban digiri na biyu kawai.

Tallafin karatu na Chevening shi ne wanda kasar Birtaniya ke daukar nauyi, ana daukewa dalibi dawaniyar karatu gaba daya, tare da ba shi damar yin karatu a manyan jami'o'in Ingila.

Ita ma Kanada ta na da nata shirin tallafin karatun mai suna VCGS. Duk da cewa dalibai daga kowace kasa za su iya nema, sai dai iya masu yin karatun digirin digirgir ne ke samu.

Akwai kuma sauran nau'ikan tallafin karatu da ba mu ambata ba, dalibai na iya yin nasu binciken a kai.

Kara karanta wannan

Jigawa: Wasu matasa 2 sun mutu a yanayi mai ban tausayi a hanyar zuwa Kasuwa

Dan Arewa ya samu tallafin karatu kyauta

A zantawarmu da Dakta Attahiru Dan-Ali Mustapha, wani matashi daga Arewa da ya taba cin gajiyar tallafin, ya yi magana bayanin yadda ya yi karatu kyauta a Ingila.

Dakta Attahiru ya wayar da kan daliban Najeriya masu son yin karatu a kasashen waje kan matakan da za su iya bi domin samun tallafin yin karatu kyauta a waje.

Tattaunawarmu, ta mayar da hankali kan abubuwa hudu: Abin da dalibi ke bukata kafin neman tallafin, dabarun cike tallafin, matsalolin da dalibai ke fuskanta da shawarwarin bakon namu.

1. Sai dalibi na da hanya zai samu tallafi?

Dalibai da dama na fargabar cewa irin wanna tallafi na kasar waje na bukatar hanya kafin a samu. Sai dai Dakta Attahiru ya ce ko kadan, mutum ba ya bukatar taimakon kowa.

"Kamar ni, ban san kowa ba, ni ne na cike tallafin, na gabatar da dukkanin takardun da ake bukata, kuma Allah ya sa na tsallake tantancewar da aka yi."

Kara karanta wannan

Makarantun jihohi 22 da NELFund ta kara tantancewa a ba dalibai aron kudin karatu

Kasancewar tallafi ne da kasashen duniya ke bayarwa, ana amfani da cancanta ne ba hanya ba, kuskure ne dalibi ya sanya a ransa cewa sai yana da hanya zai samu tallafin karatu a waje.

2. Wadanne takardu dalibi zai tanada?

Dakta Attahiru ya yi nuni da cewa jami'o'in kasashen waje na da bukatu ko kuma ka'idojin da suke kafawa kafin ba dalibai gurbin karatu, kuma sai ka samu gurbin ne za ka samu tallafi.

Daga cikin abubuwan da jami'o'i ke nema akwai takardar shaidar kammala digirin farko ko hadi da na biyu, akwai bukatar dalibi ya samu takardar shaidar yabo daga malamai da wurin aiki.

Kasancewar kasashen da aka fi samun tallafin na amfani da Turanci wajen koyarwa, Dakta Attahiru ya ce akwai makarantun da ke bukatar dalibi ya yi jarabar IELTS da zai nuna ya iya Turanci.

Amma abin da ya fi muhimmanci shi ne, dalibi ya samu gurbin karatu a wata jami'ar kasar waje, ta hakan ne kawai zai iya samun tallafin karatu.

Kara karanta wannan

Gwamnatin tarayya ta nunka albashin ma'aikatan shari'a sau 3, Tinubu ya sanya hannu

3. Dabarun neman tallafin karatu a waje

Dakta Attahiru ya ce babban abin da ake dubawa wajen ba da tallafin karatu shi ne sakamakon da mutum ya kammala jami'a da shi, inda ya ce mafi akasari ana fara duba masu 'first class da second class upper.)

Sai dai matashin ya ce ko da dalibi bai samu shiga ajin kololuwar sakamako ba, zai iya amfani da kwarewarsa, ko kuma wani ilimi da ya koya a aikin da ya yi domin tsara takardar neman tallafin.

"Akwai lokutan da ba sakamakon karatu ake dubawa ba, ana duba kwarewa da hazakarka. Idan har ka yi rubutu mai kyau da ya nuna kai jajirtacce ne, kuma ka san me kake yi, za a iya ba ka tallafin."

Matashin ya kara da cewa, akwai bukatar dalibi ya rubuta takardar bayani kan kansa (personal statement) wadda za ta gamsar da masu ba da tallafin cewa dalibin na da duk abin da ake bukata domin ya yi karatun.

Kara karanta wannan

An shiga tashin hankali a Arewa: 'Yan bindiga sun kashe shugaban makaranta da wasu 6

4. Me zai faru ga dalibi marasa hazaka?

Dakta Attahiru ya ce ba kasafai ake samun dalibin da ya samu tallafin karatu a waje ba a same shi da gaza yin kokari saboda samun tallafin ma ba aikin rago ba ne.

Sai dai ya ce akwai makin da masu ba da tallafin ke sakawa dalibi, idan har ya gaza cimma wannan maki, to ana lalata tallafin tare da mayar da shi gida.

5. Shawarar Dakta Attahiru ga dalibai

Matashin ya ce:

"Daliban da ke son samun tallafin karatu a waje, suna da bukatar su tabbatar sun samu sakamako mai kyau tun a matakin digiri na farko. Idan dalibi zai iya cin 'first class' to ya tabbata ya ci hakan.
"Idan har ba ka gama digirin farko da sakamako mai kyau ba, to zai zama kalubale ga dalibi wajen samun tallafin karatu ko samun gurbin yin karatu a wata makarantar kasar waje."

Kara karanta wannan

'Yan majalisa sun fusata da kalaman Obasanjo, sun karyata zargin kayyade albashinsu

Dakta Attahiru ya jaddada cewa, dalibai za su samu sauki da kuma saurin samun tallafin karatu a kasashen ketare idan suka kammala digirin farko da sakamako mai kyau.

Tallafin Chevening: Damar yin karatu a Birtaniya

A wani labarin, mun ruwaito cewa an bude gurbin neman tallafin karatu na Chevening na zangon 2025/2026 wanda zai ba dalibai damar yin karatu kyauta a jami'o'in Birtaniya.

Tuni aka bude shafin da dalibai za su nemi tallafin Chevening da kuma abubuwan da ake bukata daga dalibai yayin da ake rufe neman tallafin a ranar 5 ga Nuwamba, 2024.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.