Gwamnatin Buhari ta sanar da wani sabon tallafin karatu don amfanin matasa

Gwamnatin Buhari ta sanar da wani sabon tallafin karatu don amfanin matasa

Hukumar kula da rarar kudin man fetir, PTDF ta bayyana cewa daga sati mai zuwa za ta fara karbar takardar muradi daga daliban Najeriya masu bukatar hukumar ta tallafa musu akan karatunsu, inji rahoton jaridar Daily Trust.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito hukumar na gayyatar daliban digiri na biyu da daliban digirin digirgir dasu fara aika mata takardunsu daga sati mai zuwa, ga masu sha’awar neman tallafin karatu a jami’o’in Najeriya.

KU KARANTA: Ramin karya kurarre ne: Manyan ayyukan gwamnatin tarayya guda 17 a jihar Sakkwato

Gwamnatin Buhari ta sanar da wani sabon tallafin karatu don amfanin matasa
Hukumar PTDF

Shugaban hukumar, Aliyu Gusau ne ya bayyana haka a yayin bikin rantsar da daliban digiri na biyu na digirigir da hukumar zata tura Birtaniya don karo karatu, inda yace wadanda za’a baiwa tallafin karatun a jami’o’in Najeriya zasu fi yawa fiye da na kasashen waje.

Gusau yace: “Daga sati mai zuwa zamu fara karbar bukatar daliban dake bukatar tallafin karo karatu, zamu sanar a shafukan jaridu, kuma zamu kai har watan Satumba muna sauraron mabukata.”

Sai dai Gusau ya gargadi dalibai cewa hukumar ba zata lamunci tsawaita shekarun karatu ba daga bangaren dalibai, inda tace duk wanda ya wuce shekarunsa na karatu ba zai cigaba da samun tallafin ba.

Daliban da ake rantsar wadanda za’a tura su jami’o’in kasar Ingila sun hada da daliban digiri na biyu su 122, da masu digirindigirgir su 76, haka zalika yace hukumar ta rage jami’o’in hadin giwa na kasar Ingila daga 60 zuwa 15, don inganta tsarin tallafin karatun.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng