Ba a Gama da Matsalar Matatar Fatakwal ba, NNPCL Ya Gano Haramtattun Matatu 63

Ba a Gama da Matsalar Matatar Fatakwal ba, NNPCL Ya Gano Haramtattun Matatu 63

  • Kamfanin NNPCL ya bayyana cewa ya bankado haramtattun matatun mai har 63 a yankin Neja Delta tare da bututu 19 na satar mai
  • Bayanin kamfanin na zuwa ne yayin da ake nuna damuwa kan gazawarsa na fara aikin matatar Fatakwal yayin da Agusta ke karewa
  • NNPCL ya sanar da cewa ya kuma gano wata rijiyar mai da ta lalace a Bayelsa tare da kama danyen man da aka sata a Ribas

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Kamfanin mai na kasa (NNPCL) ya ce ya bankado tare da kwace mai daga wasu haramtattun matatun mai guda 63 a cikin makon da ya gabata.

Wani rahoton binciken kamfanin na ranar Laraba, ya ce a cikin makon da ya gabata, an gano haramtattun bututun mai guda 19 da kuma matatun mai guda 63 a yankin Neja Delta.

Kara karanta wannan

Arangama tsakanin manoma da makiyaya ta jawo asarar rayuka a Adamawa

NNPCL ta yi magana kan haramtattun matatun mai da ta gano a yankin Neja Delta
NNPCL ya gano haramtattun matatu da bututun mai a yankin Neja Delta. Hoto: @nnpclimited
Asali: Facebook

NNPCL ya sanar da wannan ci gaban ne a lokacin da ake tsaka da damuwa kan gaza fara aikin matatar mai ta Fatakwal kamar yadda kamfanin ya alkawarta, inji rahoton Channels.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

NNPCL ya gaza fara aikin matatar Fatakwal

Matatar mai ta Fatakwal da ke karkashin kulawar kamfanin NNPCL a jihar Ribas ya sake fuskantar matsalar da ta tilasta jinkirta lokacin fara aikinsa, a karo na shida.

Ma’aikatar albarkatun man fetur ta tarayya da NNPCL sun yi alkawarin fara aikin matatar a cikin wannan wata, amma babu alamar fara tace mai a daidai lokacin da watan ke shirin karewa.

A watan Yuli, shugaban kamfanin na NNPCL, Mele Kyari, ya bayyana karara cewa matatar man Fatakwal za ta fara aiki a farkon watan Agusta.

NNPCL ya bankado haramtattun matatun mai

Sai dai a wani yunkuri na nuna kokarin da ya ke yi na yaki da satar danyen mai, jaridar Leadership ta ruwaito kamfanin ya ce an gano wasu haramtattun matatun mai guda 63.

Kara karanta wannan

Tinubu ya kuma gamuwa da cikas bayan kwace jiragen fadar shugaban kasa 3 a ketare

A cikin makon da aka yi nazari a kai, an gano bututun mai guda 19 na satar mai, yayin da wasu kuma aka gyara su a wurare daban-daban a jihohin Bayelsa da Rivers.

Ya kara da cewa an gano wata rijiyar mai da ta lalace a jihar Bayelsa kuma an gano danyen man da aka sata a wata ma'ajiyar mai a jihar Ribas.

Tasirin matatun man Najeriya kan farashi

A wani labarin, mun ruwaito cewa 'yan kasuwar mai sun ce akwai yiwuwar farashin man fetur ya kara tsada idan har dukkanin matatun man Najeriya suka fara aiki.

'Yan kasuwar man sun bayyana hakan yayin da gwamnatin tarayya ta yi magana kan fara aikin matatar Ribas da Fatakwal, inda suka ce canjin dala da Naira zai shafi farashin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.