Sufetan 'Yan Sanda Ya Shiga Matsala, an Kama Shi a Bidiyo Yana Cin Zarafin Jami'in KAEDCO
- An cafke wani sufetan 'yan sanda da aka kama a bidiyo yana kokarin lahanta wani ma'aikacin wutar lantarki da ya je duba wutar gidansa
- An ruwaito cewa sufetan 'yan sandan mai suna Aminu Yahaya Bidda ya yi kokarin cakawa ma'aikacin wutar wuka yayin cacar baki
- Kamfanin KAEDCO ya shigar da koke ga rundunar 'yan sanda bayan abin da ya faru, inda ya nemi a tuhumi dan sandan tare da kai shi kotu
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Kaduna - Rundunar 'yan sandan Rigasa da ke jihar Kaduna ta cafke wani jami'in dan sanda mai suna Sufeta Aminu Yahaya Bidda.
An kama Sufeta Aminu a cikin bidiyo rike da wuka yana barazana da cin zarafin wani ma'aikacin kamfanin lantarki na KAEDCO.
Jaridar Leadership ta ruwaito Sufeta Aminu wanda ya ke aiki ne da ofishin 'yan sanda na Tudun Wada da ke kwaryar Kaduna ya yi kokarin dabawa jami'in KAEDCO wuka.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
KAEDCO ta yi karar Sufeta Aminu
Kamfanin KAEDCO mai raba wutar lantarki ya kai koke ga rundunar 'yan sanda ta hannun kwamishinan rundunar na Kaduna.
Labarin da mu ka samu ya bayyana cewa kamfanin ya roki a kama Sufeta Aminu, a bincike shi tare da kai shi kotu.
KAEDCO na zargin jami'in dan sanda da cin zarafi, yunkurin kisa da kuma yi wa ma'aikacinsa barazana a lokacin da ya ke bakin aiki.
Ana so a kai 'dan sandan CID
A yayin da kamfanin ya nemi a mika lamarin ga sashen CID domin yin bincike, ya kuma nemi kwamishinan 'yan sandan jihar ya shiga lamarin domin kare lafiya da rayukan ma'aikatansa.
A cewar kamfanin KAEDCO, bincike ya nuna cewa dan sandan ya biya kudin wutar lantarkin da ya ke sha a gidansa sau biyu kawai a wannan shekara.
Bidiyo da jawabin Ganau kan lamarin
Shaidun gani da ido sun ce ma’aikacin wutar lantarki na Kaduna ya isa gidan dan sandan ne domin duba mitarsa da ake zargin tana aiki ba bisa ka'ida ba.
Lamarin ya ta'azzara cikin hanzari lokacin da jami'in ya fusata kamar yadda aka gani a wani faifan bidiyo da ya yadu a intanet, inda ya yi ta kaiwa ma'aikacin hari da wuka.
Ma'aikacin ya yi sa'a ya tsira ba tare da an jikkata shi ba, sai dai an ce wani mai wucewa da ya yi ƙoƙarin shiga tsakani ya samu raunin a ƙafarsa.
Kalli bidiyon a kasa:
An cafke dan sanda ya bindige dattijuwa
A wani labarin, mun ruwaito cewa rundunar yan sandan Jihar Adamawa ta kama wani jami'in ta bisa zargin kisa, Saja Aliyu Yusuf, dalilin mutuwar wata dattijuwa mai shekaru 80.
An ruwaito cewa jami'in dan sandan ya harbi marigayiyar lokacin da ake kokarin kama wani matashi a Doubelli, wani bangaren Jimeta da ke Yola, daren Alhamis da misalin 9:45 na dare.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng