An Kama 'Dan Sandan Bogi Dauke da Takardun Kotun Karya a Legas

An Kama 'Dan Sandan Bogi Dauke da Takardun Kotun Karya a Legas

  • Rundunar yan sandan jihar Legas ta kama wani mutum mai suna Charles Chukwudi da ke damfarar mutane da sunan aikin dan sanda
  • An kama mutumin ne dauke da kayayyakin da suka shafi aikin yan sanda da kotu da yake amfani da su wajen damfarar mutane
  • Tuni rundunar yan sandan ta dauki mataki a kan sa domin ya zama darasi ga masu ayyuka irin nasa a Legas dama fadin Najeriya

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Legas - Rundunar yan sanda a jihar Legas ta kama wani mutum mai suna Charles Chukwudi da ake zargi da zama sojan gona.

Bogi police
Am kama dan danfara mai karyar aikin dan sanda a Legas. Hoto: Nigerian Police Force
Asali: Facebook

A cikin bayanai da rundunar ta wallafa a shafinta na Facebook, ta nuna cewa Mista Charles Chukwudi yana karyar aikin dan sanda da aikin kotu.

Kara karanta wannan

Filato: Adadin mutanen Zurak da suka mutu a harin 'yan bindiga ya karu

Har ila yau rundunar ta kama mutumin dauke da kayayyakin da suka kebanta da ayyukan kotu da aikin dan sanda.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kayan da aka samu hannun 'dan sandan'

Rundunar yan sanda ta bayyana cewa an kama Charles dauke da hatimin kotuna da dama ciki har da kotunan da ke Yaba da Epe.

An kuma kama shi da katin shaidar aikin dan sanda na bogi da fasfo sanye da kayan aikin yan sanda da ya hada.

Ayyukan da 'dan sandan bogin yake yi

Rundunar yan sandan ta tabbatar da cewa ana zargin mutumin yana amfani kayayyakin bogin ne domin damfarar mutane.

Charles Chukwudi ya shahara da ayyukan damfara a cikin garin Legas ta inda har an taba nemansa ruwa a jallo.

Kama mai karyar aikin 'yan sanda

Rahoton da jami'an yan sanda suka fitar ya nuna cewa an kama Charles Chukwudi ne a jiya Laraba, 22 ga watan Mayu.

Kara karanta wannan

Shaye shaye: Mahaifi ya bukaci kotu ta daure dansa a jihar Kano

Ba tare da wata-wata ba kuma rundunar yan sanda ta gurfanar da shi a gaban kotu domin bincike da yanke masa hukuncin da ya dace.

'Yan sanda sun hallaka yan bindiga

A wani rahoton, kun ji cewa rundunar ƴan sandan jihar Bauchi ta tabbatar da samun nasara kan ƴan bindiga da ake zargi da yin garkuwa da mutane domin kuɗin fansa a jihar.

Jami'an rundunar tare da haɗin gwiwar mafarauta sun yi nasarar hallaka ƴan bindiga mutum takwas tare da ceto mutum uku sa suka yi garkuwa da su.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng

Online view pixel