Ladanin Masallacin Landan da aka kai wa hari da wuka yace ya yafe duniya da lahira

Ladanin Masallacin Landan da aka kai wa hari da wuka yace ya yafe duniya da lahira

- Ladanin wani babban masallaci a London da aka sokawa wuka a wuya da baya ya ce ya yafewa wanda ya kai mishi harin

- Wani mutum ne mai shekaru 29 ya samu ladanin da ya dau shekaru 30 yana kiran sallah a masallacin ya soka mishi wuka a wuya da baya

- Kamar yadda Ladanin ya bayyana, ya yafewa mutumin kuma a halin yanzu yana matukar tausayin bawan Allah din saboda kaddara ce ta gibto

Ladanin da wani mutum ya soka wa wuka a wuya yayin da yake kiran sallah ya bayyana cewa ya yafewa wanda ya kai mishi harin.

Raafat Maglad, wanda yake cikin shekarunshi na 70 ya baro asibitin da aka kaishi a London sannan ya dawo masallacin da yake kiran sallah, kasa da sa’o’i 24 bayan an soke shi da wuka.

Wani mutum mai shekaru 29 na hannun ‘yan sanda bayan an zargeshi da yunkurin kashe ladani a wani masallalci da ke London.

Ladanin Masallacin Landan da aka kai wa hari da wuka yace ya yafe duniya da lahira
Ladanin Masallacin Landan da aka kai wa hari da wuka yace ya yafe duniya da lahira
Asali: Facebook

Tare da ciwon da kuma yadda likitoci suka rufe wajen a wuyan ladanin, Maglad ya sanar da manema labarai cewa “na yafewa mishi. Kuma ina matukar tausaya mishi. Abinda ya faru ya riga ya faru kuma ba za a iya mayar da hannun agogo baya ba. Mutum ne shima kuma abinda ya faru kaddara ne.”

Kamar yadda jaridar Independent.uk ta ruwaito, mai kiran sallan an soke shi da wuka ne wajen karfe 3 na rana a wani hari da wani mutum ya kai mishi.

KU KARANTA: Bussa Krishna: Mutumin da ya dauki shugaban kasar Amurka Donald Trump a matsayin ubangiji

Maglad wanda asalinshi dan kasar Sudan ne yace, ya taba ganin maharin a masallacin yana bauta.

A yayin bayani kan yadda harin ya kasance, ya ce: “Muna sallah ne kawai naji wani ya make ni ta baya. Ban ce komai ba kawai sai ganin jini nayi yana zuba daga wuyana. Daga nan aka garzaya dani asibiti. Komai ya faru a gaggauce ne.”

Maglad wanda ya kasance mai kiran sallah a masallacin na shekaru 30 ya ce, a matsayin shi an Musulmi, ba zai tsani kowa ba kuma yana da matukar amfani ya halarci sallar Juma’a.

“Idan na rasa Sallah, toh nayi rashi babba. Tana da matukar amfani garemu Musulmai,” Ya kara da cewa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel