Kekere Ekun: NJC Ta Bukaci Tinubu Ya Nada Mace a Matsayin Shugabar Alkalan Najeriya

Kekere Ekun: NJC Ta Bukaci Tinubu Ya Nada Mace a Matsayin Shugabar Alkalan Najeriya

  • Majalisar shari'a ta kasa (NJC) ta nemi Shugaba Bola Tinubu da ya nada Kudirat Kekere-Ekun a matsayin shugabar alkalan Najeriya
  • A cewar wata sanarwa, NJC ta gabatar da sunan Kekere-Ekun yayin da wa'adin alkalin alkalai, Olukayode Ariwoola zai kare 22 ga Agusta
  • Legit Hausa ta tattaro cewa majalisar shari'a ta kasar ta kuma gabatar da sunanyen alkalai 27 domin nada su alkalan manyan kotuna

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja – Majalisar shari’a ta kasa (NJC) ta ba da shawarar a nada Mai shari’a Kudirat Motonmori Kekere-Ekun a matsayin shugabar alkalan Najeriya (CJN).

Idan har aka tabbatar da nadin Mai Shari’a Kekere-Ekun, za ta gaji Mai shari’a Olukayode Ariwoola, wanda wa'adinsa ke karewa a ranar 22 ga watan Agusta, 2024.

Kara karanta wannan

NEC: Ana rade radin kwace kujerar Ganduje, APC ta tsaida ranar taron da ake jira

Majalisar shari'a (NJC) ta nemi Tinubu ya nada Kekere-Ekun matsayin shugabar alkalan Najeriya
Kudirat Kekere-Ekun: Mace ta biyu da ake so ta zama shugabar alkalan Najeriya. Hoto: @njcNig
Asali: Twitter

NJC na so Kekere-Ekun ta zama CJN

Jaridar The Nation ta ruwaito cewa alkalin alakai shi ne shugaban sashen shari'a na gwamnatin Najeriya, kuma shi ne yake jagorantar kotun kolin kasar da kuma majalisar shari'a (NJC).

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wannan ne karo na biyu da Najeriya za ta iya samun shugabar alkalai mace, tun bayan da aka nada Aloma Mariam Mukhtar GCON a mukamin a 2012.

Majalisar shari'a ta kuma gabatar da sunan wasu alkalai 27 domin a nada su alkalan manyan kotunan jihohi, kamar yadda sanarwa daraktan yada labarain NJC, kungiyar Soji Oye ta nuna.

NJC ta wallafa sunayen alakali 27 da ake nema a nada a matsayin alkalan kotunan jihohi da kuma wanda za a nada a matsayin Kadi na kotun shari’ar Abuja a shafinta na intanet.

Alkalai 6, babbar kotun jihar Kwara

Kara karanta wannan

Abubuwan da suka wakana a taron Tinubu da tsofaffin shugabannin Najeriya a Aso Rock

  • Olawoyin, Ibijoke Olabisi
  • Dikko, Yusuf Adebayo
  • Osuolale-Ajayi, Temitope Olalekan
  • Adeniyi, Oluwatosin Adenike
  • Abdulrazaq, Fatimah Funsho
  • Folorunsho, Oba Muritala

Alkalai 4, babbar kotun jihar Benue

  • Kor, Vincent Tersoo
  • Tor, Damian Tersugh
  • Adagba, Nguhemen Julie
  • Ikwulono, Maigida Maimuna

Alkali 1, babbar kotun jihar Kaduna

  • Zubairu, Murtala Ja’afaru

Alkalai 8, babbar kotun jihar Rivers

  • Obu, Ibietela Innocent Madighi
  • Onyiri, Frank
  • Ugoji, Victor Chinedum
  • Fubara, Alatuwo Elkanah
  • Kokpan, Bariyima Sylvester
  • Obomanu, Godswill Vidal
  • Oguguo, Rita Chituru
  • Wifa-Adedipe, Lesi

Alkalai 2, kotun daukaka kara ta al’ada, Benue

  • Igba, Theophilus Terhile
  • Onche, Ogah Inalegwu

Alkalai 6, babbar kotun jihar Ondo

  • Fabuluje, Adewumi William
  • Ogunwumiju, Mobayonle Idowu
  • Daomi, Williams Adebisi
  • Demehin-Ogunbayo, Inumidun Happiness
  • Adegoroye, Olufunke Adeola
  • Kpemi, Ojufisintei Justinah

Khadi 1, kotun daukaka kara ta shari’a, Abuja

Muhammad, Lawal Munir

Ariwoola: An rantsar da alkalin alkalai

Kara karanta wannan

Majalisar magabata: Buhari, Jonathan sun magantu kan yadda Tinubu ke mulkin Najeriya

A wani labarin mun ruwaito cewa a ranar 27 ga watan Yuni, 2022 aka rantsar da Olukayode Ariwoola a matsayin sabon shugaban alkalan Najeriya (CJN).

An nada Mai shari'a Ariwoola matsayin alkalin alkalan kasar ne biyo bayan murabus din CJN Tanko Mohammad daga babbar kujerar shari'a ta Najeriya.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.