Bata Al'adar Hausawa: Masu Kafafen Yada Labaran Arewa Sun Kai Karar Arewa24

Bata Al'adar Hausawa: Masu Kafafen Yada Labaran Arewa Sun Kai Karar Arewa24

  • Ƙungiyar masu kafafen yaɗa labarai ta Arewa (NBMOA) ta kai ƙarar tashar Arewa24 a gaban hukumomin Najeriya
  • Ƙungiyar ta zargi tashar da gudanar da shirye-shiryen da suka ci karo da al'ada da addinin al'ummar Hausawa na Arewacin Najeriya
  • NBMOA ta buƙaci hukumomin da su hana tashar ci gaba da gudanar da harkokinta a ƙasar nan saboda saɓa dokar da ta yi

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum da nishaɗi

FCT, Abuja - Ƙungiyar masu kafafan yaɗa labarai ta Arewa (NBMOA) ta shigar da ƙara a hukumance kan kamfanin Network Arewa24 Ltd, masu gudanar da tashar talabijin ta Arewa24.

Ƙungiyar ta zargi gidan talabijin da yin kaka-gida a kasuwannin yaɗa labarai na Arewacin Najeriya da kuma yin wasu abubuwa da suka saɓawa al-adar malam-bahaushe.

Kara karanta wannan

Atiku ya caccaki Tinubu, ya bayyana inda gwamnatinsa ta samu matsala

An kai karar Arewa24
Kungiyar NBMOA ta kai karar Arewa24 Hoto: Ahmed Tijjani Ramalan, Arewa24
Asali: Facebook

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ina aka kai ƙarar Arewa24?

An miƙa ƙorafin ne ga hukumar kare hakkin masu amfani da kayayyaki da abokan hulɗa ta ƙasa (FCCPC), hukumar kula da watsa labarai ta ƙasa (NBC), da hukumar kula da tallace-tallace ta Najeriya (ARCON).

A wata sanarwa da kwamitin amintattu na ƙungiyar NBMOA ya aikowa Legit Hausa a ranar 12 ga watan Agusta, ta yi zargin tashar Arewa 24 TV, wacce aka sani da Network Arewa24 Limited, tana gudanar da aiki ba tare da cikakken lasisi ba daga hukumar NBC.

Sanarwar na ɗauke da sa hannun shugaban gudanar da ƙungiyar, Dr. Ahmed Tijjani Ramalan.

Ana zargin Arewa24 da bata al'adar Hausa

NBMOA ta koka kan cewa tashar tare da haɗin gwiwar kamfani Lens 54 LLC wanda ke da hannun jari a cikinta, suna yin abin da bai dace ba ga al'adun Hausawa na Arewacin Najeriya.

Kara karanta wannan

Zaben 2027: Dan majalisa ya fara shirin yadda APC za ta kwato Kano a hannun NNPP

Ƙorafin ya yi zargin cewa waɗanda suka kafa tashar da darektocinta waɗanda ke zaune a ƙasar Amurka, ba su da masaniya kan al'adun Arewa.

Wannan ya sanya suke samar da shirye-shirye da suka ci karo da al'ada da addinin mutanen yankin.

Me ƙungiyar take so hukumomin su yi a kai?

Ƙungiyar ta buƙaci hukumar FCCPC da ta dakatar da tashar Arewa 24 daga yin kaka-gida kan haƙƙoƙin abokan hulɗa a masana'antar yaɗa labarai.

NBMOA ta buƙaci hukumar NBC da ta hana tashar Arewa24 watsa shirye-shiryenta saboda rashin yin rajista.

Ƙungiyar ta kuma buƙaci hukumar ARCON da ta hana tashar saka tallace-tallace.

Arewa24 ta fito da sababbin shirye-shirye

A wani labarin kuma, kun ji cewa Arewa24 ta sanar da samar da sabon fannin samar da shirye-shiryen wasan kwaikwayo da fina-finai.

Tashar za ta tsara, ta rubuta, ta kuma samar da wasu sababbin shirye-shiryen wasan kwaikwayo da ke ba da labarin ingantattun abubuwan Afirka daga Arewacin Najeriya da Afirka ta Yamma a cikin harshen Hausa da turanci.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng