Zaben 2027: Dan Majalisa Ya Fara Shirin Yadda APC Za Ta Kwato Kano a Hannun NNPP
- Ɗan majalisar wakilai mai wakiltar Doguwa/Tudun Wada, Alhassan Ado Doguwa, ya fara shiri kan babban zaɓen shekarar 2027
- Doguwa ya sha alwashin kawowa APC nasara a Kano a 2027 inda ya buƙaci a ba shi muƙamin shugaban yaƙin neman zaɓen
- 'Dan siyasar ya yi martani ne bayan wani ɗan majalisa na NNPP ya bayyana shi a matsayin matsala ga jam'iyyarsa ta APC
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Kano - Ɗan majalisar wakilai daga jihar Kano, Alhassan Doguwa, ya sha alwashin karɓo jihar Kano ta dawo hannun jam'iyyar APC a babban zaɓe na 2027.
Alhassan Ado Doguwa ya ce zai tabbatar da cewa jam’iyyar APC ta samu nasara a babban zaɓen 2027 da ke tafe nan gaba.
Doguwa na son APC ta ƙwace Kano
Ɗan majalisar ya buƙaci a bar shi ya zama darakta-janar na yaƙin neman zaɓen jam’iyyar APC a 2027 a jihar Kano, cewar rahoton jaridar Aminiya.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Jaridar The Punch ta ce Doguwa ya bayyana haka ne a Abuja ranar Lahadi, yayin da yake mayar da martani kan iƙirarin da wani ɗan majalisa, Abdulmumini Jibrin ya yi na cewa yana barazana ga jam’iyyar APC a jihar.
Abdulmumin Jibrin Kofa na jam'iyyar NNPP ya kuma ce Doguwa matsala ne siyasance ga jam’iyyarsa ta APC.
"Ina so na yi amfani da wannan dama domin na nuna girmamawa ga shugabannin jam’iyyarmu da su ba ni dama na yi jagoranci wajen zama darakta-janar na yaƙin neman zaɓen jihar Kano a 2027."
"Ni ba matsala ba ne a siyasance a Kano. Ni kadara ce, abin alfahari ga jam’iyyar APC a matakin jiha da kuma ƙasa."
- Alhassan Ado Doguwa
Doguwa shi ne ɗan majalisar wakilai ɗaya tilo da aka zaba a ƙarƙashin jam’iyyar APC a yankin Kano ta Kudu a zaɓen 2023.
Kano: Doguwa ya caccaki Jibrin Kofa
A wani labarin kuma, kun ji cewa shugaban kwamitin majalisar wakilai mai kula da albarkatun man fetur, Alhassan Doguwa ya mayar da martani ga Abdulmumin Jibrin Kofa.
Alhassan Ado Doguwa ya mayar da martanin ne bisa zargin cewa ya ci mutuncin tsohon gwamnan jihar Kano kuma jagoran jam'iyyar NNPP, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng