Gaskiyar abinda ya faru tsakaninmu da Arewa24 a kan shirin Labarina, Malam Aminu Saira

Gaskiyar abinda ya faru tsakaninmu da Arewa24 a kan shirin Labarina, Malam Aminu Saira

- A wata zantawa da aka yi da Malam Aminu Saira, darakta a masana'antar Kannywood ya bayyana yadda ya fara bada umarni

- Malam Aminu ne darektan fim din nan mai dogon zango, Labarina, inda ya sanar da dalilan da yasa suka dakatar da nuna fim din

- A cewar Saira, yanzu haka suna jiran su kammala zango na 3 da na 4 kafin su zauna su yi yarjejeniyar da Arewa24

A wata tattaunawa da Aminiya tayi da fitaccen daraktan masana'antar Kannywood, Malam Aminu Saira, ya bayyana yadda ya fara bayar da umarni a fitaccen fim dinsa mai dogon zango, Labarina.

Ya bayyana cewa ba wata matsala bace ta faru tsakaninsu da Arewa 24 kamar yadda wasu suke zato don sun daina haska fim din Labarina. Ya ce sun kammala nuna zango na 1 da na 2, kuma dama su kadai suka yi yarjejeniya. Sai sun kammala zango na 3 da 4 tukunna su zauna dasu. Amma ba wani sabani suka samu ba.

Saira ya kara da cewa, suna iyakar kokarin ganin cewa shirin zango na 3 da 4 sun fi na baya ingantuwa ta kowanne bangare.

KU KARANTA: Mu 'yan uwan juna ne, Tsohon gwamnan Zamfara ya ziyarci Shasha

Dalilin da yasa na dade ina jan zare na a Kannywood, Darakta Aminu Saira
Dalilin da yasa na dade ina jan zare na a Kannywood, Darakta Aminu Saira. Hoto daga @Aminiya
Asali: Twitter

Sannan suna ganin cewa ana kulawa wurin dakatar da wasu kura-kurai da mutane suka sanar dasu akai don gudun kada hakan ya kara faruwa. Kuma ana kyautata zaton sai sun fi wadancan inganci.

Saira ya ce yadda manyan mutane suke nuna so da shaukin fim din Labarina ya sanya yake samun kwarin guiwa.

Kuma hakan yana tabbatar musu da cewa abinda ake yi a Labarina yana gamsar da al'umma. Don haka wajibi ne a kara rike sana'arsu da muhimmanci.

Saira ya kara da bayyana yadda har farfesoshi suka tattauna dashi akan fim din, inda ya bukaci idan sun ga akwai kura-kurai su yi magana.

KU KARANTA: Kwamishina a Zamfara yayi murabus, ya ce APC za ta kwace kujerar Matawalle

A wani labari na daban, tsohon ministan sufurin jiragen sama kuma jigo a jam'iyyar PDP, Femi Fani-Kayode ya sanar da gwamnatin tarayya da ta bar 'yan Najeriya su dinga daukar makamai idan har ta bar Fulani suna yawo da AK47 domin kare kansu da shanunsu.

Kamar yadda yace, idan aka duba lamarin ta haka toh dole ne a baiwa jama'a damar yawo da makamai domin bai wa kansu kariya daga 'yan bindiga da kuma makiyayan, Vanguard ta ruwaito.

Ya ce hanyar da ta fi dacewa wurin shawo kan matsalar tsaron kasar nan shine dukkan matakai na gwamnati su hada karfi da karfe kuma a hana 'yan Najeriya yawo da makamai.

Aisha Khalid ma'aikaciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018.

Ta kwashe shekaru biyu tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu.

Za a iya bibiyar Aisha a shafinta na Twitter @DiyarKatsinawa

Asali: Legit.ng

Online view pixel