'Yan Bindiga Sun Kashe Kyaftin Ibrahim, Jarumin Sojan Najeriya Ya Rasa Rayuwarsa

'Yan Bindiga Sun Kashe Kyaftin Ibrahim, Jarumin Sojan Najeriya Ya Rasa Rayuwarsa

  • Rahotanni sun bayyana cewa wasu 'yan bindiga sun kashe kyaftin din soja, Kyaftin Ibrahim Yohana watanni 9 bayan aurensa
  • Ibrahim Yohana wanda ya fito daga jihar Kaduna an ce ya kasance soja mai hazaka wanda ke shiga gaba wajen kare 'yan kasarsa
  • Ana ganin mutuwar Kyaftin din wata manuniya ce ta irin hatsarin da sojojin Najeriya ke fuskanta kullum a wajen yaki da matsalar tsaro

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Wasu ‘yan bindiga sun kashe Kyaftin Ibrahim Yohana, wani jajirtaccen sojan Najeriya dan asalin jihar Kaduna.

Labarin mutuwarsa na zuwa ne watanni tara kacal da aurensa, wanda ya bar iyalinsa, abokansa, da abokan aikinsa cikin makoki.

'Yan bindiga sun kashe jajurtaccen sojan Najeriya, Kyaftin Ibrahim Yonaha
Kyaftin Ibrahim Yohana: 'Yan bindiga sun yi ajalin sojan Najeriya. Hoto: @ZagazOlaMakama
Asali: Twitter

An yi jimamin mutuwar sojan Najeriya

Kara karanta wannan

An shiga jimami a Arewacin Najeriya, mata da miji da 'ya'yansu 5 sun mutu bayan cin rogo

Fitaccen mai sharhi kan lamuran tsaro a yankin Tafkin Chadi, Zagazola Makama ya wallafa labarin mutuwar jarumin sojan a shafinsa na X.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cewar Makama, abokan aikin Kyaftin Ibarahim, sun bayyana shi a matsayin wanda ya shahara da jarumtaka da jajircewa wajen yi wa kasarsa hidima.

Makama ya ce mutuwar Kyaftin Ibrahim na nuni da irin hatsarin da sojojin ke fuskanta a yakin da suke yi da kalubalen tsaro a kasar.

"Mun rasa jarumi" - Abokin Kyaftin Ibrahim

"Mun sake rasa wani jarumin soja," a cewar wani abokin mamacin wanda ya nuna baƙin ciki sosai da mutuwar Yohana wanda ya ce ya sadaukar da rayuwarsa wajen hidimtawa kasa.

Iyalin sojan, waɗanda suka nuna tsantsar murna a lokacin aurensa watanni da suka shude, yanzu sun fada cikin jimami da zaman makokin rashin ɗansu, ɗan’uwa kuma miji da suke ƙauna.

Kara karanta wannan

Ana rade radin gwamnan PDP zai sauya jam'iyya, tsageru sun jefa 'bam' ofishin APP

An ce abokan aikin Kyaftin Ibarahim sun bayyana shi a matsayin babban jami’i mai hazaka wajen gudanar da aikinsa wanda yake shiga a gaba wajen kare rayukan jama'a.

Mutuwarsa ba rashi ne kawai ga danginsa da abokansa ba, amma ga daukacin al'ummar Najeriya, a cewar Makama.

An kashe babban soja da jami'ai 2

A wani labarin, mun ruwaito cewa 'yan bindiga sun kashe babban jami'in soja da ya kai matsayin kyaftin da wasu sojoji biyu a yankin Sabo, shiyyar Funtua a jihar Katsina

Sanata mai wakiltar Katsina ta kudu (shiyyar Funtua), Muntari Ɗandutse ne ya bayyana haka, inda ya ce 'yan ta'adda sun addabi shiyyar da kashewa da kuma sace mutane.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.