Kisan Sojoji 17: Wani Soja Ya Sha Alwashin Daukar Fansa Kan Ta'asa a Delta, Ya Koka

Kisan Sojoji 17: Wani Soja Ya Sha Alwashin Daukar Fansa Kan Ta'asa a Delta, Ya Koka

  • Yayin da ake jimamin mutuwar sojoji a jihar Delta, wani soja ya sha alwashin daukar fansa kan wadanda suka yi kisan
  • Sojan wanda ya ce shi ma dan asalin jihar Delta ne ya nuna damuwa kan yadda ya karanta martanin mutane kan mutuwar sojojin
  • Ya ce dole za su dauki fansa kan abin da aka yi wa ‘yan uwansu ganin yadda suke sadaukar da rayuwarsu kan kare Najeriya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Delta – Wani soja mai suna Egitanghan G. ya bayyana cewa za su dauki fansa kan kisan sojoji da aka yi a jihar Delta.

Sojan wanda shi ma ya fito daga jihar Delta ya ce abin takaici ne yadda wasu ke munanan kalamai ga sojojin da suka mutu.

Kara karanta wannan

Kisan sojoji 16: Majalisar Dattawa tana ganawar sirri da hafsoshin tsaro, an samu bayanai

Soja ya sha alwashin daukar fansa kan kisan 'yan uwansu a Delta
Wani soja dan jihar Delta ya ce za su dauki fansa kan kisan 'yan uwansu da aka yi a jihar Delta. Hoto: Defence Headquarters.
Asali: Twitter

Wane mataki sojan zai dauka?

Egitanghan ya nuna damuwa kan yadda abin ya faru duk da sadaukar da rayukansu da suke yi wurin kare kasar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cikin wani faifan bidiyo da aka wallafa a TikTok a jiya Laraba 20 ga watan Maris, sojan ya tura sako ga ‘yan uwansa da ke Neja Delta.

Punch ta ruwaito sojan na cewa:

“Yayin da na ke karanta martanin jama’a kan mutuwar sojojin, kuka kawai na ke yi saboda nima dan jihar Delta ne.”
“Ni na san abin da na ke fuskanta kan kare kasar Najeriya, na shafe shekaru hudu a Maiduguri, sojoji suna mutuwa saboda kasarsu.”

- Egitanghan G

Soja ya ce ba za su yafe ba

“Amma har kun samu karfin hali da za ku kashe mana ‘yan uwa a jihar Delta sanna ‘yan Kudu maso Kudu kuna martani na abin takaici.”

Kara karanta wannan

Yadda rikicin gona ya yi sanadin kashe sojoji 17 a jihar Delta, in ji shugaban al'umma

“Ba za mu yafewa duk wanda ya kashe mana sojoji ba, dole za mu dauki mataki, duk da nima dan Warri ne, na so ace ina cikin wadanda za su yi aikin.”

- Egitanghan G

Wannan martani na sojan na zuwa bayan kisan wasu sojoji 17 a kauyen Okuoma da ke karamar hukumar Ughelli ta Kudu a jihar Delta.

Daga bisani, Majalisar Dattawa ta yi ganawar sirri da dukkan hafsoshin tsaro domin fara bincike kan lamarin.

Sojoji sun kona kauye a Delta

Kun ji cewa ana zargin wasu fusatattun sojoji sun dauki mataki kan kauyen Okuoma da ke jihar Delta a Kudancin Najeriya.

Sojojin sun kona kauyen ne da aka hallaka musu jami’ai 17 a makon da ya gabata wanda ya ta da hankulan jama’a a kasar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel