Walson Jack: Tinubu Ya Rantsar da Sabuwar Shugabar Ma’aikatan Gwamnatin Tarayya
- Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya rantsar da Esther Walson-Jack a matsayin sabuwar shugabar ma’aikatan gwamnatin tarayya
- An ranstar da Walson-Jack ne a taron majalisar zartarwa ta tarayya (FEC) da Shugaba Tinubu ya jagoranta a yau Litinin, 12 ga Agusta
- Rantsar da Walson-Jack ya biyo bayan karewar aikin shugabar mai barin gado, Folasade Esan wadda ta rike mukamin tun daga 2019
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja - Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya rantsar da sabuwar shugabar ma’aikatan tarayya, Misis Didi Esther Walson-Jack.
Hakan na zuwa ne yayin da majalisar zartarwa ta tarayya (FEC) ta gudanar da taron bankwana da yin jinjina ga shugabar ma’aikatan mai barin gado, Dakta Folasade Esan.
Da yake jawabi a lokacin rantsarwar, gabanin fara taron FEC, Tinubu ta shaida wa Didi Walson-Jack cewa za ta dauki wani babban nauyi da Misis Esan ta sauke, inji rahoton Daily Trust.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Shugaban ya kuma yi addu’ar Allah ya yi wa sabuwar shugabar ma’aikatan jagora yayin da za ta fara jagorantar ma'aikatan tarayyar.
Wacece Didi Esther Walson-Jack?
Idan ba a manta ba, shugaba Tinubu ya amince da nadin Walson-Jack a matsayin shugabar ma’aikatan gwamnatin tarayya, a ranar 17 ga Yuli, 2024.
Tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari ya fara nada Esther ne a shekarar 2017, kuma ta yi ayyuka da dama a matsayin babbar sakatariya.
Ita ce matar tsohon babban sakataren hukumar NBA kuma jigo a fannin koyar da al'umma, Hon. Nimi Walson-Jack.
Yemi Esan ta yi kalaman bankwana
Jaridar Vanguard ta ruwaito cewa tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari ya nada Yemi-Esan a matsayin shugabar ma’aikatan tarayya a ranar 18 ga Satumba, 2019.
Da take magana a wani taro wanda kungiyar JUNC ta shirya domin karrama ta, tare da yi mata bankwana daga aikin gwamnati, Yemi-Esan ta ce:
“Na gode wa Ubangiji da ya ba ni damar yi wa kasata hidima. Ban taba mafarkin zama shugabar ma’aikatan tarayya ba, wannan ikon Allah ne.
"Ina godiya ga tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari da Shugaba Bola Tinubu da suka saukaka aikina."
Buhari ya yi wa Oyo-Ita murabus
Tun da fari, mun ruwaito cewa shugaba Muhammadu Buhari ya yi wa Winifred Ekanem Oyo-Ita ritaya daga shugabar ma'aikatan tarayya daga ranar Alhamis 27 ga Fabrairun 2020.
Hakan na zuwa ne watanni biyar bayan Buhari ya dakatar da Oyo-Ita daga kujerarta a kan zargin rashawa ta hanyar bayar da kwangiloli ta ofishinta ba bisa ka'ida ba.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng