PCACC Ta Bankado N18bn da wasu 'Yan Siyasar Kano Suka Wawure, Rimingado Ya Magantu

PCACC Ta Bankado N18bn da wasu 'Yan Siyasar Kano Suka Wawure, Rimingado Ya Magantu

  • Muhuyi Magaji Rimingado ya bayyana cewa hukumar PCACC ta bankado yadda 'yan siyasa ke amfani da ma'aikata suna satar kudin jama'a
  • Rimingado, shugaban hukumar PCACC mai yaki da rashawa a Kano ya ce sun gano N18bn da 'yan siyasa suka sata tare da taimakon ma'aikata
  • Shugaban ya fadi hakan ne a wani taron bita kan dokokin yaki da rashawa da mu'amala da kudin gwamnati da aka shiryawa ma'aikatan Kano

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Kano - Shugaban hukumar karbar korafe-korafen jama'a da yaki da rashawa ta Kano (PCACC), Muhuyi Magaji Rimingado ya yi sabuwar fallasa kan cin hanci da rashawa a jihar.

Muhuyi Rimingado ya ce 'yan siyasa na amfani da ma'aikatan gwamnatin jihar suna satar kudaden jama'a.

Kara karanta wannan

Bayan mayar da shi kotu, Ganduje ya fadi abin da za a yi wa bangaren shari'a

Shugaban PCACC ya yi magana kan 'yan siyasar Kano da ke wawure kudin gwamnati
Kano: Rimingado ya ce PCACC ta gano N18bn da 'yan siyasa suka sace. Hoto: Muhuyi Magaji Rimingado.
Asali: Facebook

PCACC ta bankaɗ N18bn na sata a Kano

Shugaban PCACC ya ce hukumar zuwa yanzu ta bankaɗo Naira biliyan 18 da wasu 'yan siyasa suka wawure ta hanyar amfani da wasu ma'aikatan jihar, inji rahoton Daily Trust.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Rimingado ya bayyana hakan ne a wani taron karawa juna sani da hukumar PCACC ta shirya tare da hadin guiwar ofishin shugaban ma'aikatan Kano karkashin shirin (ROLAC II)

Shugaban hukumar yaƙi da rashawar ya ce:

"Ana kama ma'aikatan da laifin karbar rashawa dumu dumu, don haka muka ga bukatar yiwa ma'aikatan gwamnati wannan bita domin gujewa dadin bakin 'yan siyasa masu rashawa.
"Kashi 90 na rashawa da ake tafkawa na faruwa ne a lokacin da 'yan siyasa za su sayi kayayyaki kuma da ma'aikata ake hada baki hakan ta faru."

PCACC ta yiwa ma'aikatan Kano bita

Kara karanta wannan

Zanga zanga: Matashi a Kano ya yi barazanar kashe kakakin rundunar 'yan sanda

Jaridar This Day ta ruwaito Muhuyi Rimingado ya ce taron zai ilmantar da ma'aikatan gwamnati dokokin da suka shafi sayo kayayyaki da tafiyar da kudin gwamnati.

"Za mu ba su ilimi kan yadda za su tafiyar da kudin jihar Kano da kuma kiyaye dokokin yaki da cin hanci da rashawa a yayin gudanar da ayyukansu.
"Mun hada da ma'aikatan kananan hukumomi saboda su ma 'yan siyasa na amfani da su wajen satar kudi. Su ke ciro kudin, su kaiwa 'yan caji sannan a kaiwa 'yan siyasar don samu lada."

Kotu ta umarci a sallami Rimingado

A wani labarin, mun ruwaito cewa Babbar Kotun Tarayya da ke zamanta a jihar Kano ta yi zama kan tuhume-tuhume da ke kan Muhuyi Magaji Rimingado.

Kotun ta dauki matakin ne saboda saba umarnin kotu da Muhuyi Magaji Rimingado ya yi bayan wasu mutane biyu sun shigar da korafi kansa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.