“Wawaye ne”: Malamin Addini Ya Dura kan Mata Masu Kwalliya Ranar Aure, Ya yi Gargadi

“Wawaye ne”: Malamin Addini Ya Dura kan Mata Masu Kwalliya Ranar Aure, Ya yi Gargadi

  • Babban shugaban cocin RCCG, Fasto Enoch Adeboye ya ce matan da ke yin kwalliya da fente fuskarsu a lokacin bikinsu wawaye ne
  • Fasto Adeboye ya bayyana hakan ne a yayin wani babban taron ministocin cocin RCCG da ya gudana a kan titin Legas zuwa Ibadan
  • Malamin addinin ya ce matan da ke yin kwalliya lokacin bikinsu suna nuna cewa sun raina yadda ubangiji ya halicce su tun farko

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Babban shugaban cocin RCCG, Fasto Enoch Adeboye ya caccaki matan da suke yin kwalliya kafin biki da kuma lokacin bukukuwan aurensu.

Fasto Adeboye ya ce irin wadannan matan wawaye ne kuma sun nuna cewa za su yi gyara ga yadda ubangiji ya tsara halittarsu tun kafin aurensu.

Kara karanta wannan

Malamin addini ya fadi dalilin kasa magance cin hanci, ya kawo mafita a Najeriya

Shugaban cocin ECCG ya ce matan da ke kwalliya ranar aure wawaye ne
Fasto Enoch Adeboye ya ce mata masu kwalliya ranar aure sun raina halittar Ubangiji. Hoto: Hearst Newspapers, PeopleImages
Asali: Getty Images

Malamin addinin ya yi magana ne a lokacin taron ministocin RCCG a babban taronta na ka sa da ya gudana a titin Legas-Ibadan, inji rahoton PM News.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Fasto ya caccaki mata masu kwalliyar biki

Shugaban cocin ya nuna takaicinsa kan yadda irin wadannan matan suke bayyana rashin imaninsu ga Allah da ya halicce su a yadda suke.

A cewar Fasto Adeboye:

“Wasunku suna son su zama kamar wasu nau'ikan mutanen duniya. Ina shiga damuwa sosai idan ina tuna wasu abubuwan da nake gani yanzu.
“Mutane suna kashe dubban daruruwan naira wajen yin hotuna. Sannan a ranar daurin aure yarinyar ta sanya kayan ado iri-iri da shafe fuskarta da fenti.
"Matan da ke yin kwalliya su ne wadanda ba su yarda da halittarsu da ubangiji ya yi ba. Lokacin da aka halicce ku, ubangiji ya kama tsara surarsu bisa hikimar tsari."

Kara karanta wannan

'Ƴan bindiga sun yi garkuwa da babban malamin addinin Musulunci a Arewacin Najeriya

"Ku je biki ba kwalliya" - Fasto ga mata

Daily Post ta ruwaito Fasto Adebayoye ya ce daga lokacin da mace ta fara yin kwalliya, tana tunanin za ta iya yiwa halittar ubangiji kwaskwarima, to daga nan ta zama wawa.

"Babu wanda zai iya cin ubangiji gyara a halittar da aka yi masa. Wanda ya ce zai fenti fuskarsa to ya zama wawa."

Malamin addinin ya bukaci masu zuwa ibada cocinsa da su rika zuwa wajen aurensu a yadda ubangiji ya yi su ba tare da sun yi wani shafe-shafe da sunan kwalliya ba.

Amarya ta cire kwalliya, aure ya mutu

A wani labarin, mun ruwaito cewa wani Balarabe ya saki amaryarsa bayan da ta wanke kwalliyar fuskarta a karon farko tsawon lokacin da suka dade suna shan soyayya.

An ce Dakta Abdul Azeez Azif Asaf mai shekara 34 ya rabu da amaryar sa ‘yar shekara 28 bayan da ya ga fuskarta da ta koma tamkar bakuwa gare shi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.