Wani mutumi ya rabu da Amaryar sa bayan ta cire kayan shafa

Wani mutumi ya rabu da Amaryar sa bayan ta cire kayan shafa

- Wani Balarabe ya rabu da ‘Yar Amaryar sa jim kadan bayan daura aure

- Angon yace ya gano ashe Amaryar ta sa ba ta da kyau idan ta cire kwalliya

- Wannan mutumi yace yaudarar sa aka yi da kyale-kyale da ja-girar karya

Wani mutumi ya rabu da Amaryar sa bayan ta cire kayan shafa

 

 

 

 

 

Wani Balarabe ya saki ‘Yar Amaryar matar sa jim kadan da yin aure bayan ya gan ta ba tare da kwalliya ba a karo na farko. Dakta Abdul Azeez Azif Asaf mai shekara 34 ya rabu da amaryar sa ‘Yar shekara 28 bayan da ya ga fuskar ta ba tare da kayan shafa ba.

Dakta Abdul Azeez Azif yace Amaryar ta yaudare sa da kayan shafe-shafe. Asalin abin da ya wakana dai shine, ango Abdul Azeez ya kai matar sa teku domin wasa da ruwa, ko da ta shiga ta fito sai ya ga abubuwa sun canza, ba dai kamar yadda ya saba ganin ta ba. Yace bayan ruwa ya wanke mata fuska sai ya ga kamar ba ita ba.

KU KARANTA: Emmanuel Adebayor ya musulunta

Abdul Azeez Azif yace ashe Amaryar ta sa tana sanya gashin ido da girar karya ne sannan kuma an yi mata aiki domin a rikida mata siffa kafin tayi aure. Yace sam bai gane Amaryar ba ko da ta shi ga ruwa ta fito.

Likitan wannan Amaryar yace tayi niyyar fadawa mijin ta abin da ya faru, sai dai ta makara. Yanzu haka dai sun rabu, mijin yace fau-fau ba zai yarda ba. [GULF news]

 

 

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel