Jami’an Tsaro Sun Cafke Wanda Ya Dage a Tsige Matashin da Tinubu Ya ba Mukami

Jami’an Tsaro Sun Cafke Wanda Ya Dage a Tsige Matashin da Tinubu Ya ba Mukami

  • Alkaseem Nuhu Abdulkadir ya soki mukamin da shugaban kasa ya dauka ya ba Abdul Hameed Yahaya Abba
  • ‘Dan gwagwarmayar ya yi ikirarin Arewa maso gabas ba ta wani amfana da kujerar da Abdul Don Jazzy yake kai
  • Ana cikin haka sai aka ji jami’an tsaro sun yi ram da Alkaseem Abdulkadir, Don Jazz ya ce babu hannunsa a ciki

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada

Bauchi - A wata wasika da ya rubuta zuwa ga shugaban kasa, Alkaseem Nuhu Abdulkadir ya bukaci Bola Tinubu ya kori hadiminsa.

Alkaseem Nuhu Abdulkadir ya na ganin Abdul Hameed Yahaya Abba wanda aka fi sani da Abdul Don Jazzy bai amfani da gwamnati.

Abdul Don Jazzy
Akwai masu kiran Bola Tinubu ya tsige Abdul Don Jazzy daga kujerarsa Hoto: Alkaseem Nuhu Abdulkadir / Olusegun Dada
Asali: Facebook

Ana so a tsige Abdul Don Jazzy

Kara karanta wannan

"Yadda Buhari, Kyari suka hana ni mallakar rijiyoyin mai ": Fitaccen dan kasuwa

A wata budaddiyar wasika da Malam Alkaseem Nuhu Abdulkadir ya rubuta a Facebook, ya ce hadimin shugaban kasar ya saki layi.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A wasikar, ya nuna Abdul Don Jazzy ya yi watsi da bukatun al’ummar Arewa maso gabas, ba ya taimaka masu kuma bai kawo wani cigaba.

Shugaban na kungiyar Northern initiative for Growth yana ganin cewa mai taimakawa shugaban kasar bai san aikin da ke kan sa ba.

Wasikar ba ta tsaya nan ba, an zargi matashin da amfani da mukamin wajen fifita bukatun kan shi a lokacin da talakawa su ke kuka.

Bola Tinubu zai canza Abdul Don Jazzy?

Saboda haka ne Alkaseem Nuhu Abdulkadir ya huro wuta cewa a mutanensu sun cancanci wakilcin wanda zai rike amanarsu da kyau.

A shafinsa na X, Sanruk Musa ya bayyana yadda wannan wasika ta jawo martani mai zafi.

Kara karanta wannan

Zanga zanga: Tsohon gwamnan Kano ya gano bakin zaren, ya aika saƙo ga Tinubu

Abdul Don Jazzy ya maida martani

Mai taimakawa shugaban kasar ya yi bidiyo a matsayin raddi, yana wanke kan shi daga zargin da ‘dan gwagwarmayar yake yi masa.

Abdul Don Jazzy ya yi jero ayyukan alherin da ya kawowa Arewa maso gabas duk da cewa ba a ware wasu kudi ga ofishin nasa ba.

An kama mai sukar hadimin Tinubu

Amma Abdul Yello ya sake magana, ya dage cewa wannan bawan Allah bai san aikinsa ba kuma bai inganta rayuwar jama’a ba.

Daga yin wannan bidiyo sai Legit Hausa ta ji labari cewa an cafke shi, a ranar Juma’a ya sanar a shafinsa cewa ya bar hannun jami’an tsaro.

Hadimin shugaban kasar wanda ake tunanin yana Saudi bayan aurensa da aka yi kwanaki, ya ce babu hannunsa a abin da ya faru.

Kira ga gwamnatin Bola Tinubu

Mun kawo labari na musamman cewa musulmai daga cikin matasa su na so su nemi tallafin jari, amma gwamnati ta cusa ruwa a ciki.

Ganin yadda aka sa riba a NYIF, ana kira ga ‘yan majalisar tarayya da sauran manyan gwamnati su kawo bashin da musulmai za su mora.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng