Yunwa na Barazana ga Rayukan Almajiran Kano, An Roki Matasa Su Hakura da Zanga Zanga

Yunwa na Barazana ga Rayukan Almajiran Kano, An Roki Matasa Su Hakura da Zanga Zanga

  • Mabarata da ke samun na abinci a kan titunan jihar Kano sun bayyana matsin rayuwar da suka shiga sakamakon zanga-zanga
  • Sun bayyana yadda zanga-zangar ke barazana ga rayuwarsu, inda suka roki matasa da su hakura da su tattauna da gwamnati domin maslaha
  • A zantawarmu da Auwal Bala, wani shugaban matasa a jihar Katsina, ya ce zanga-zangar ta shafi har masu sana'a ba almajirai kadai ba

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Kano - Wasu almajirai a kan titunan Kano sun yi kira ga masu zanga-zangar yunwa da ake yi a fadin kasar nan da su hakura hakanan domin maslahar jama'a.

Wannan kiran na zuwa ne yayin da aka shiga rana ta takwas a ranaku 10 da matasa suka ware domin gudanar da zanga-zangar adawa da tsadar rayuwa a fadin kasar.

Kara karanta wannan

Kano: Mabarata sun shafe kwanaki da yunwa, sun nemi a janye zanga zanga

Almajirai sun yi magana kan yadda zanga-zanga ta shafi rayuwarsu a Kano
Kano: Almajira sun nemi a kawo karshen zanga-zanga saboda rashin abinci. Hoto: PIUS UTOMI EKPEI/Contributor
Asali: Getty Images

Almajirai sun koka kan rashin samun abinci

Jaridar Daily Trust ta ruwaito wani Baba Haliru, mai shekaru 70 da ke yin bara a Rigiyar Zaki, ya bayyana cewa rayuwa ta yi matukar wahala ga almajirai sakamakon zanga-zangar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya koka da cewa:

“Mu 14 ne a gidana, kwana biyu daga cikin kwanaki 4 da aka sanya dokar hana fita ba mu ci komai ba. Ba abinci sai dai ruwa kawai muke sha.
"Don Allah a tuntubi wadanda suka shirya zanga-zangar nan, su taimaka su kawo karshenta ta hanyar tattaunawa da gwamnati."

Wasu mabarata sun sake nanata maganar Haliru, inda suka yi kira da a kawo karshen zanga-zangar da kuma dage dokar hana fita baki daya.

Zanga-zanga na barazana ga rayuwar almajirai

Malama Mario Kabiru ta rukunin gidajen Hotoro ta ce:

“Kayyakin abinci sun kare kuma ba za mu iya fita mu sayi kari ba. Ba mu da kuɗi, kuma ba za mu iya ci gaba da jure wannan yanayi ba.

Kara karanta wannan

"An yi abin kunya", Rundunar soja ta yi tir da masu sata a wuraren ibada ana zanga zanga

Malam Isa Musa na unguwar Dorayi ya kuma yi kira ga gwamnati da ta bullo da matakan da za su dace da bukatun tsofaffi marasa galihu, inji rahoton The Punch.

“Muna bara ne saboda ba mu da wanda zai tallafa mana. Tun bayan sanya dokar hana fita, ba mu ci abinci ba tsawon kwana uku, hakan barazana ne ga rayuwarmu."

Zanga zanga ba almajirai kadai ta shafa ba

A zantawarmu da shugaban matasan garin Daudawa da ke jihar Katsina, Auwal Bala, ya ce zanga-zanga ba wai almajirai kadai ta shafa ba, har wadanda ke da sana'ar yi.

Auwal Bala ya ba da misalin yadda aka tilasta mutane rufe shagunansu saboda dokar zaman gida, abin da ya ce ya jawo karewar kayan abinci ko kayan cefane ga iyalai da dama.

Shugaban matasan ya ce maimakon a ci gaba da zanga-zanga yayin da marasa galihu ke galabaita saboda rashin abinci, zai fi kyau a koma teburin sasanci da gwamnati.

Kara karanta wannan

Sojoji sun karbi mulki yayin da zanga zanga ta tsananta a Bangladesh, an samu bayanai

Ya roki gwamnatin tarayya da ta jihohi da su kasance suna kawo tsare tsare da zai shafi talakan da ke cikin kauya domin shi ne ya fi kowa shan wahala idan aka hana shi fita ko da na rana daya ne.

Gombe: Almajirai za su shiga tsarin inshora

A wani labarin, mun ruwaito cewa gwamnatin Gombe ta yanke shawarar inganta rayuwar almajiran jihar ta hanyar sanya su a cikin tsarin inshorar lafiya.

Gwamantin ta bayyana cewa akwai tsare-tsaren bayar da tallafi na kiwon lafiya da za ta kawo ga kananan yara wanda almajirai za su ci gajiyar shirin a jihar.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.