“Manyan Arewa da za Su Iya Rarrashin Masu Zanga Zanga,” Masoyin Tinubu Ya Fadi Sunaye 2

“Manyan Arewa da za Su Iya Rarrashin Masu Zanga Zanga,” Masoyin Tinubu Ya Fadi Sunaye 2

  • Wani 'dan kwamitin yakin neman zaben Asiwaju Bola Tinubu ya ce akwai mutane biyu da za su iya kwantar da tarzomar zanga-zanga a Arewa
  • Jesutega Onokpasa ya bayyana cewa tsohon gwamnan Kogi, Yahaya Bello da takwaransa na jihar Kaduna, Nasir El-Rufai ne za su iya hakan
  • Sai dai Mista Onokpasa ya bayyana takaicinsa kan yadda aka mayar da tsofaffin gwamnonin saniyar ware har wasu ke jifarsu da karairayi

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Mista Jesutega Onokpasa, 'dan kwamitin yakin zaben Asiwaju Bola Tinubu, ya yi magana kan zanga-zangar yunwa da ake yi a fadin kasar nan.

Dan-a-mutun shugaban kasar ya ce "da ace ba a nunawa Yahaya Bello da Nasir El-Rufai wariya ba, da su ne za su iya kwantar da tarzomar masu zanga-zanga a Arewa."

Kara karanta wannan

Tsohon gwamna a Arewa na daukar nauyin zanga zanga? an gano gaskiya

Masoyin Tinubu ya yi magana kan wadanda za su iya rarrashin masu zanga-zanga a Arewa
Masoyin Tinubu ya fadi sunayen mutum 2 da su iya kwantar da tarzomar zanga-anga a Arewa. Hoto: Nation builder, @elrufai, @officialABAT
Asali: Twitter

Jaridar Daily Trust ta ruwaito Mista Onokpasa ya ce an juyawa tsohon gwamnan na Kogi da takwaransa na Kaduna baya yayin da ake tuhumarsu kan zarge-zarge marasa tushe.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Su wa za su iya rarrashin 'yan Arewa?

Ya ce tsofaffin gwamnonin, a halayyarsu da aka sani, da yanzu sun dauki ragamar tattaunawa da matasa a madadin Shugaba Bola Tinubu.

"Kasancewar suna da kwarewa, na tabbata da su ne za su iya rarrashin matasan, sannan su tabbata an wanzar da zaman lafiya a yankin Arewa."

Mista Onokpasa ya bayyana hakan ne a wani faifan bidiyo yayin da yake caccakar mutanen Arewa da Tinubu ya ba mukamai amma suka gaza kare gwamnatinsa yayin zanga-zangar.

A cewar lauyan, da yawa daga cikin wadanda aka ba mukamai daga Arewa ba sa kaunar Shugaba Tinubu kuma ba sa goyon bayan gwamnatinsa, inji rahoton Vanguard.

Kara karanta wannan

Zanga zanga: Iyalan matashin da aka kashe a Kano sun mika bukata 1 ga gwamnati

Onokpasa ya caccaki masu mukaman Arewa

Ya kara da cewa ba abin da masu mukaman Arewa ke yi sai kara gogawa Yahaya Bello da Nasir El-Rufai kashin kaji ta hanyar jifarsu da karairayin da har yanzu ba su kawo hujja ba.

"Su ne ke ikirarin cewa El-Rufai, Yahaya Bello da ma ministan tsaro, Bello Matawalle ne suke daukar nauyin zanga-zanga kuma sune suke da hannu da daga tutocin rasha da ake yi.
"Maimakon su da suke da mukamai su yi kokarin dawo da zaman lafiya a Arewa, sun koma suna jifar masu karfin fada aji da munanan karairayi wadanda sun gaza kawo hujja."

- Jesutega Onokpasa

Yahaya Bello na da hannu a zanga-zanga?

A wani labarin, mun ruwaito cewa tsohon gwamnan Kogi, Yahaya Bello ya fito ya kare kansa yayin da wasu ke zargin yana daga cikin wadanda ke daukar nauyin zanga-zangar da ake yi.

Yahaya Bello ya musanta zargin da ake yi masa inda ya ce zai dauki matakin shari'a kan wadanda ke yada karairayin musamman wani dan gwagwarmaya, Jackson Ude.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.