Rundunar Soji Ta Dauki Mataki kan Sojan da Ya Kashe Ɗan Shekara 16 a Garin Zariya

Rundunar Soji Ta Dauki Mataki kan Sojan da Ya Kashe Ɗan Shekara 16 a Garin Zariya

  • Rundunar sojojojin Najeriya ta cafke sojan da aka ce ya kashe wani karamin yaro dan shekara 16 a Samarun Zariya a ranar Talata
  • Idan ba a manta ba, mun ruwaito cewa jami'in soja ya yi harbi a layin Sarkin Pawa da ke Samarun Zariya inda ya samu yaro a makogoro
  • Wata sanarwa da rundunar sojin ta fitar ta ce tuni aka tura tawagar manyan jami'an soji zuwa gidansu yaron domin yi masu ta'aziyya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Rundunar sojojin Najeriya ta yi magana kan kashe wani yaro Ismail Muhammad dan shekara 16 da wani soja ya yi a layin Sarkin Pawa, Samaru Zariya a jihar Kaduna.

Kara karanta wannan

Bidiyo: Bayanai sun fito da soja ya harbe 'dan shekara 16 har lahira a garin Zariya

Rundunar ta ce ya zuwa yanzu dai ta cafke sojan da ya kashe yaron kuma ana yi masa tambayoyi yayin da ta aika tawaga zuwa gidansu yaron domin ganawa da iyayensa.

Sojoji sun yi magana kan kashe yaro dan shekara 16 a garin Zariya
An kama sojan da ya harbe yaro dan shekara 16 har lahira a garin Zariya. Hoto: Saidu Shehu, NigerianArmy
Asali: Facebook

Manjo Janar Onyema Nwachukwu, daraktan hulda da jama'a na rundunar sojin ne ya sanar da haka a sanarwar da rundunar ta fitar a shafinta na X.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Abin da ya kai sojoji Samaru Zariya

Sanarwar ta bayyana cewa dakarun soji sun samu sakon gaggawa cewa wasu 'yan daba sun taru a Samaru Zariya suna kona taya a kan titi da jifar jami'an tsaro da dutse.

Sanarwar ta kara cewa nan da nan dakarun suka shirya suka tafi inda abin ke faruwa domin tarwatsa 'yan daban tare da tabbatar da dokar zaman gida da gwamnatin jihar ta sanya,

Abin da ya jawo soja ya kashe Ismail

Kara karanta wannan

"An yi abin kunya", Rundunar soja ta yi tir da masu sata a wuraren ibada ana zanga zanga

A cewar sanarwar:

"Da isowar jami'anmu wurin, ’yan daban suka yi yunkurin kai wa sojojin farmaki, lamarin da ya sa wani soja ya yi harbin gargadi domin tsorata ’yan daban.
"Sai dai kuma kaddara ta riga fada, inda aka samu akasi harsashin ya samu wani yaro dan shekara 16 mai suna Ismail Mohammed.
"Tuni aka cafke sojan da ya yi harbin kuma ana yi masa tambayoyi ya zuwa lokacin da aka fitar da wannan rahoton."

Sojoji sun tura tawaga zuwa Samaru

Sanarwar ta ce hafsan sojojin, Laftanal Janar Taoreed Abiodun Lagbaja ya nuna takaicinsa kan abin da ya faru inda ya tura tawaga zuwa gidansu mamacin.

Onyema Nwachukwu ya ce babban kwamandan rundunar ta 1, Manjo Janar Lander Saraso ne zai jagoranci tagawar dakarun sojoji zuwa ta'aziyya da jajantawa iyalan Ismail.

Sanarwar ta kuma kara da cewa tuni aka yi wa Ismail sutura kamar yadda addinin Musulunci ya tanada, inda har wasu manyan jami'an soji suka halarta.

Kara karanta wannan

An gano inda masu zanga zanga ke samun tallafin kudi, 'yan sanda sun dauki mataki

Soja ya harbe yaro dan shekara 16

Tun da fari, mun ruwaito cewa wani soja ya harbe wani yaro dan shekara 16, Ismail Mohammed har lahira a layin Sarkin Pawa, Samarun Zariya a jihar Kaduna a ranar Talata.

Rahotanni sun ce sojan ya yi harbi har sau biyu inda harsasan suka ratsa kofar gidansu Ismail, daya ya samu yaron a makogoro wanda ya fadi kasa matacce.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.