Soja ya buɗe wa ƙananan yara wuta a kusa da fadar shehun Borno, ya kashe ɗaya

Soja ya buɗe wa ƙananan yara wuta a kusa da fadar shehun Borno, ya kashe ɗaya

Wani soja mai suna Bukar Mustapha Limanti da ke aiki tare da Operation Lafiya Dole ya kashe wani yaro mai shekaru 9 a Maiduguri, jihar Borno.

The Cable ta ruwaito cewa an kashe yaron ne bayan Limanti ya bude wuta a kusa da fadar Shehun Borno a ƙaramar hukumar Shehuri ta jihar Borno a ranar Talata.

Wasu yara guda biyu sun samu raunuka kamar yadda rahotanni suka bayyana.

Soja ya buɗe wa ƙananan yara wuta a kusa da fadar shehun Borno, ya kashe ɗaya
Soja ya buɗe wa ƙananan yara wuta a kusa da fadar shehun Borno, ya kashe ɗaya. Hoto daga The Cable
Source: UGC

Wata majiya da abin ya faru a idon ta ta ce dama sojan ya yi ƙaurin suna wurin yin harbe harbe babu dalili a unguwar.

Kuma haka sidan ya fara harbe harbe wadda hakan ya yi sanadin rasuwar wani yaro mai shekaru 9 mai suna Abdu Tijjani.

Ya ce an kai sauran yaran biyu da suka yi rauni zuwa asibitin ICRC da ke Borno a Maiduguri don basu kulawa yayin da shi kuma sojan ya tsere.

"Wannan harbe harben ba zai rasa nasaba ba da kisar gillar da aka yi wa wani mutumin da bai ji ba bai gani ba," in ji majiyar.

DUBA WANNAN: Akwai yiwuwar ƴan ta'adda za su koma neman mambobi ta hanyar yanar gizo - Buhari

"Bukar Mustapha Limanti yaron direban Limamin jihar Borno na yanzu ne kuma yana aiki ne a sansanin ƴan gudun hijira da ke Channel a hanyar Maiduguri zuwa Gubio.

"Duk safe ya kan tafi wurin aikinsa ya dawo yana fitinar mutane cikin dare da bindigarsa AK 47.

"Makonni biyu da suka wuce ya harbe kare da akuya a Shehuri. Hakan yasa Digima Zubairu, Dagajin Shehuri ta arewa ya masa gargadi amma duk da haka ya cigaba da harbe harben."

Wata majiya daga asibitin kwararrun na Maiduguri ta nemi a sakayya ta tace yara biyun suna samun sauƙi.

Majiyar ta ce wani abu mai kama da wannan ya faru a kwanakin baya inda wani soja ya harbe wani kurma mai sayar da goro a nan unguwar.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel