“Garin Kwaki Ya fi Karfin Talaka”: Tsohuwar Shugabar NDDC ta Tsagewa Tinubu Gaskiya

“Garin Kwaki Ya fi Karfin Talaka”: Tsohuwar Shugabar NDDC ta Tsagewa Tinubu Gaskiya

  • An yi kira ga Shugaba Bola Tinubu da ya gaggauta magance matsalar hauhawar farashin kayan abinci wadda ta kai kololuwarta a watan Yuni
  • Tsohuwar shugabar hukumar raya Neja Delta (NDDC), Ibim Semenitari ta ankararda Shugaba Tinubu cewa garin kwaki ya fi karfin talaka
  • Semenitari, wadda tsohuwar kwamishinan watsa labarai ce a Rivers ta ce ya zama wajibi Tinubu ya rika yin taka-tsan-tsan a tsare-tsarensa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Tsohuwar shugabar hukumar raya Neja Delta (NDDC), Ibim Semenitari ta nemi Shugaba Bola Tinubu da ya magance matsalar hauhawar farashin abinci.

A cewar Ibim Semenitari, hauhawar farashin kayan abincin ya kai mizanin da garin kwaki ya fi karfin talakan Najeriya ya sha ko da sau daya ne a rana.

Kara karanta wannan

Zanga zanga: Tinubu ya dauki alkawari 1 yayin da ya fallasa shirin wasu 'yan siyasa

An yi kira ga Shugaba Tinubu ya magance matsalar hauhawar farashin abinci
Tsohuwar shugabar hukumar NDDC ta aika sako ga Shugaba Tinubu kan tsadar abinci. Hoto: @NGRPresident
Asali: Twitter

"Matsalar farko ita ce ta abinci, wasu ba sa iya samun abincin a yanzu," a cewarta yayin tattaunawa da Laolu Akande a shirin Channels TV na ranar Lahadi.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Garin kwaki ya fi karfin talaka" - Ibim

Semenitari, wadda tsohuwar kwamishinan watsa labarai ce a jihar Rivers ta ce 'yan Najeriya na bukatar daukin gaggawa, inda ta ce akwai bukatar wani ya kawo dauki.

Ta ce ya zama wajibi shugaban kasar ya rika yin taka-tsan-tsan a yayin da zai kawo wani tsari ga 'yan kasar, tana mai nuni da cewa:

"Dole shugaban kasar ya rika tunanin tsare-tsarensa: 'Idan na gama mulki, da me za a rika tuna ni?' Kuma gaskiyar magana ita ce, hadimansa ba za su iya bashi wannan amsar ba.
"A halin yanzu 'yan Najeriya ba sa iya cin abinci. Ba wai ina magana akan cin abinci sau uku a rana ba, ko abinci sau daya a yanzu yana gagarar mutane, garin kwaki ya fi karfin talaka."

Kara karanta wannan

Bayan gwamna a Arewa ya ki albashin N70,000, NLC ta fadi matakin da za ta dauka

Hauhawar farashin kayayyaki ta kai 34.19%

Tsohuwar kwamishiniyar ta ce kamata ya yi ace Tinubu ya nuna kwarewar mulki ba wai ya kwashi kudin kasar ya sayi sabon jirgin sama ba a lokacin da ake fama da tsadar rayuwa.

Hauhawar farashin kayayyaki a Najeriya ya kai kololuwarsa a watan Yuni, inda ya kai 34.19% kamar yadda alkaluman hukumar NBS ya nuna.

Farashin kayan abinci ya tashi zuwa 40.87% a watan Yunin 2024 sabanin 40.66% da yake a watan Mayun 2024, kuma an samu karin 15.62% da kuma 25.25% da farashin yake a Yuni da Mayun 2023.

Kalli tattaunawar a nan kasa:

Tinubu ya fallasa masu shirya zanga-zanga

A wani labarin, mun ruwaito cewa shugaban kasa Bola Tinubu ya yi ikirarin cewa akwai wasu tsirarun mutane da suka dauki nauyin zanga-zangar da ake yi domin cimma manufar siyasa.

Shugaban kasar ya ce lallai ba zai zura idanuwa ya kyale wadannan 'yan jari hujjar su wargaza zaman lafiyar kasar ba inda ya jaddada alwashin kare rayuka da dukiyoyin jama'a.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.