Kwana 1 da Zanga Zanga, Gwamnatin Tinubu Ta Bude Kofa kan Bukatun Talakawa

Kwana 1 da Zanga Zanga, Gwamnatin Tinubu Ta Bude Kofa kan Bukatun Talakawa

  • Gwamnatin tarayya ta yi magana a karon farko bayan matasan Najeriya sun fara zanga zangar adawa da tsadar rayuwa a jihohin ƙasar nan
  • Ministan Abuja, Nyesom Ezonwo Wike ne ya yi kira ga matasan Najeriya domin neman hanyar kawo karshen zanga zangar baki daya
  • Wike ya bayyana wa matasan Najeriya muhimmancin da birnin tarayya ke da shi da kuma yadda ya kamata su yi zanga zanga a cikinsa

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Gwamnatin tarayya ta fito da hanyar shawo kan matasan Najeriya da suka fara zanga zangar adawa da tsadar rayuwa.

A jiya Alhamis ne matasa a kusan dukkan sassan Najeriya suka fita kan tituna domin nuna fushinsu ga gwamnatin tarayya.

Kara karanta wannan

"Jami'an tsaro sun gano sanata mai daukar nauyin zanga zanga," Minista Wike ya yi magana

Ministan Abuja
Ministan Abuja ya yi kira ga masu zanga zanga. Hoto: Nyesom Ezonwo Wike - CON, GSSRS
Asali: Facebook

Jaridar Vanguard ta ruwaito cewa ministan harkokin birnin tarayya, Nyesom Wike ne ya yi kira ga matasan game da zanga zangar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamnati ta nemi sulhu bayan zanga zanga

Ministan na Abuja, Nyesom Ezonwo Wike ya bukaci matasan Najeriya su hakura da zanga zanga su dawo teburin sulhu.

The Nation ta wallafa cewa Nyesom Wike ya ce gwamnati ta shirya ta saurari matasan Najeriya da kuma yi musu bayani kan abin da ba su fahimta ba a tsare-tsarensu.

Wike ya yabi masu zanga zanga a Abuja

Yayin da yake magana a jiya Alhamis, Nyesom Wike ya yabi matasan da suka yi zanga zanga a Abuja wajen rashin lalata kayan gwamnati da al'umma.

Ministan ya yi kira ga matasan a kan kar su yarda da duk wanda zai lalata Najeriya da sunan zanga zanga.

Kara karanta wannan

Yadda matasa suka daƙile yunkurin ministan Tinubu a filin zanga zanga

Wike: 'Abuja na da muhimmanci sosai'

Nyesom Wike ya bayyana cewa birnin tarayya Abuja na da muhimmanci sosai ga tarayyar Najeriya a matsayinta na babban birni a kasar.

Tsohon gwamnan na jihar Ribas ya ce idan matasa suka lalata birnin tarayya da sunan zanga zanga lamarin zai shafi duk kasa baki daya.

NBA za ta taimakawa matasa a zanga zanga

A wani rahoton, kun ji cewa kungiyar lauyoyin Najeriya (NBA) ta fitar da sanarwa ta musamman kan masu zanga zangar adawa da tsadar rayuwa.

Kungiyar NBA ta dauki aniyar ba masu zanga zangar adawa da tsadar rayuwa kariya a harkar shari'a idan aka tauye musu hakkinsu ko abin ya kai ga shari'a.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng