'Yan Sandan Kano Sun Yi Harbi, Masu Zanga Zanga Sun Sa Wuta a Kofar Gidan Gwamnati

'Yan Sandan Kano Sun Yi Harbi, Masu Zanga Zanga Sun Sa Wuta a Kofar Gidan Gwamnati

  • A yau Alhamis, 1 ga watan Agusta aka wayi gari da fara zanga zangar adawa da tsadar rayuwa a dukkan jihohin Najeriya
  • A Kano, wasu masu zanga zangar sun nufi gidan gwamnati inda suka fara kone konen taya a kofar gidan gwamantin jihar
  • Legit ta tattauna da wani matashi da ya fita zanga zanga a Gombe inda ya bayyana yadda lamarin ya gudana a jihar

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Kano - Hankula sun tashi yayin da matasa masu zanga zangar adawa da tsadar rayuwa su ka tayar da wuta a kofar gidan gwamnatin jihar Kano.

Rahotanni na nuni da cewa wasu daga cikin matasa masu zanga zangar adawa da tsadar rayuwa ne suka fara kona taya a kofar gidan gwamantin.

Kara karanta wannan

Jihohin Arewa da aka sanya dokar hana fita ta awa 24 sun kai 4, an samu cikakken bayani

Jihar Kano
Jami'an tsaro sun fatattaki masu zanga zanga a Kano. Hoto: Legit
Asali: Original

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa jami'an tsaro da suke gidan gwamnatin sun dauki matakin gaggawa kan matasan.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Zanga zanga a gidan gwamnatin Kano

Matasa daga sassa daban daban na jihar Kano sun nufi gidan gwamnatin jihar yayin zanga zanga.

An ruwaito cewa matasan sun taru a kofar gidan gwamnatin ne domin jiran gwamna Abba Kabir Yusuf ya yi musu bayani.

An tada wuta a gidan gwamnati

Rahotanni sun nuna cewa matasan sun hada taya, su ka hura wuta wanda wajen ke kokarin murtukewa da hayaki.

Wasu daga cikin matasan sun cinna wuta ne a lokacin da suke tunkarar gidan gwamnatin jihar Kano a safiyar yau.

Zanga zanga: Yan sanda sun dauki mataki

Biyo bayan hura wutar, yan sanda sun dauki matakin tarwatsa matasan wajen harbi sama da harba musu barkonon tsohuwa.

Daga nan dai matasan suka fice da gudu a gigice ba tare da samun shiga gidan gwamnatin jihar ba.

Kara karanta wannan

Zanga zanga: Gwamna Abba Kabir Yusuf ya gano dalilin tashin hankali a Kano

Legit ta tattauna da Mamman Nahuta

Mamman Nahuta ya zantawa Legit cewa lamari ya birkice yayin da suka fita zanga zanga a jihar Gombe.

Matashin ya ce kamar yadda ya faru a Kano, a Gombe ma matasa sun tayar da fitina da sace sace da kyar ma suka dawo gida saboda yan sanda sun cika tituna.

Zanga zanga: NBA za ta taimakawa matasa

A wani rahoton, kun ji cewa kungiyar lauyoyin Najeriya (NBA) ta fitar da sanarwa ta musamman kan masu zanga zangar adawa da tsadar rayuwa a ƙasar nan

Kungiyar NBA ta dauki aniyar ba masu zanga zangar adawa da tsadar rayuwa kariya a harkar shari'a idan hukumomi suka tauye musu hakkinsu.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng