Zanga Zanga: Hankula Sun Tashi Bayan Jami'in Tsaro Ya Harbi Kansa
- Wani jami'in hukumar shige da fice ta ƙasar nan ya harbi kansa bisa kuskure yayin da ake gudanar da zanga-zanga kan tsadar rayuwa
- Jami'in tsaron ya harbi kansa sau uku ne lokacin da yake aiki domin hana masu zanga-zanga shiga cikin birnin Maiduguri a Borno
- An garzaya da shi zuwa asibiti domin ba shi agajin gaggawa bayan wannan tsautsayin da ya ritsa da shi kamar yadda labari ya zo
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Borno - An samu hargitsi a unguwar Bulumkutu da ke Maiduguri bayan wani jami'in hukumar shige da fice (NIS) ya harbi kansa sau uku a ƙafa.
Jami'in ya yi harbin ne bisa kuskure lokacin da yake aikin tare mutanen da suka fito domin gudanar da zanga-zanga.
Jami'in tsaro ya yi harbi bisa kuskure
Jaridar Leadership ta rahoto cewa ƙarar harbe-harben ya harzuƙa masu zanga-zangar bisa tunanin cewa ɗaya daga cikinsu aka harba, amma hankula sun kwanta bayan sun fahimci abin da ya faru.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Tawagar jami'an tsaron haɗin gwiwa da ta haɗa da ƴan sanda, sojoji, DSS, NIS, NSCDC sun kulle mahaɗar layin dogo ta Bulumkutu domin hana masu zanga-zangar shiga birnin Maiduguri.
Yunkurin tarwatsa 'yan zanga-zanga
Jami’in da ya raunata kansa yana cikin tawagar jami’an tsaro da aka tura domin tarwatsa gungun masu zanga-zangar da suka fito.
Jami’in wanda ba a bayyana sunansa ba, an garzaya da shi asibitin da ke kusa domin yi masa magani, kuma a halin yanzu ba a san halin da yake ciki ba.
Karanta wasu labaran kan zanga-zanga
- 'Yan sanda sun bayyana tagomashin da masu zanga zanga za su samu, sun kafa sharadi
- Yan sanda sun sha sabon alwashi kan zanga-zanga bayan nasarar gwamnati a kotu
- IGP ya umarci ƴan sanda su ɗauki mataki mai tsauri kan abubuwa 2 lokacin zanga-zanga
Ƴan sanda sun kora masu zanga-zanga
A wani labarin kuma, kun ji cewa zanga-zangar adawa da tsadar rayuwa a jihar Bauchi ta tarwatse yayin da jami'an ƴan sanda suka watsa barkono mai sa hawaye kan waɗanda suka fito.
Tun farko dai masu zanga-zangar sun taru ne a ƙofar fadar Sarkin Bauchi. inda suka nemi a yi masu iso domin su gana da mai martaba sarki.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng