Zanga Zanga Ta Barke a Kano Ana Daf da Fita Ta Gama Gari, Bayanai Sun Fito

Zanga Zanga Ta Barke a Kano Ana Daf da Fita Ta Gama Gari, Bayanai Sun Fito

  • Kungiyar Ja'oji da ke goyon bayan Shugaba Bola Tinubu ta gudanar da zanga-zanga domin kalubalantar masu fita gobe
  • Mambobin kungiyar sun taru ne a farfajiyar Meena Event Centre inda suke nuna damuwa kan illolin zanga-zanga a rayuwa
  • Wannan na zuwa ne yayin da ake shirin fita zanga-zanga a gobe Alhamis 1 ga watan Agustan 2024 har zuwa kwanaki 10

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Kano - Daruruwan mutane a jihar Kano sun fito kan tituna inda suke adawa da zanga-zangar da za a yi a gobe.

Mutanen sun cika titunan birnin ne a yau Laraba 31 ga watan Agustan 2024 domin nuna rashin goyon baya ga zanga-zanga.

Kara karanta wannan

"Ka samar mana da motoci": Masu zanga zanga sun tura bukatunsu ga gwamna

An gudanar da zanga-zangar nuna goyon baya ga Bola Tinubu a Kano
Kungiyar Ja'oji a Kano ta gudanar da zanga-zangar goyon bayan Tinubu. Hoto: Legit.
Asali: Original

Zanga-zanga: Kungiya ta fadi shirin Bola Tinubu

The Nation ta tattaro cewa masu zanga-zangar sun hadu ne Meena Event Centre wanda kungiyar Ja'oji ta shirya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kungiyar da ke goyon bayan Shugaba Bola Tinubu ta tabbatar da cewa shugaban yana kokarin kawo sauki a kasar baki daya.

Nasiru Bala Ja'oji wanda ya yi jawabi ga dandazon jama'a ya ce akwai matsaloli tattare da yin zanga-zanga a yanzu.

Zanga-zanga: An zargi shirin miyagu a lamarin

A wani faifan bidiyo da @jrnaib2 ya wallafa, Ja'oji ya ce akwai makircin da wasu suka shirya yayin zanga-zangar wurin kawo rigima da lalata shirin Tinubu.

"Mun yi fatali da wannan lamari, ba mu goyon bayan duk wani zanga-zanga a wannan lokaci da muke bukatar cigaban kasa da hadin kai."

- Nasiru Bala Ja'oji

Kano: Jigon APC ya gargadi masu zanga-zanga

Kara karanta wannan

Awanni kafin fita tituna, APC a Kano ta roki matasa alfarma kan lamarin zanga zanga

A wani labarin, kun ji cewa jigon jam'iyyar APC a jihar Kano ya roki 'yan jihar da su guji fitowa zanga-zanga da ake shirin yi a fadin kasar.

Nasiru Bala Ja'oji ya ce nuna damuwa kan tsare-tsaren gwamnati ba matsala ba ne amma ta hanyar rigima bai kamata ba.

Wannan na zuwa ne yayin da matasa a Najeriya ke shirin fita zanga-zanga a gone Alhamis 1 ga watan Agustan 2024.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.