NYIF: Matasan da Suka Nemi Tallafin N110bn Sun Kai 80000, An Samu Bayanai Bayan Awanni

NYIF: Matasan da Suka Nemi Tallafin N110bn Sun Kai 80000, An Samu Bayanai Bayan Awanni

  • Awanni 72 da bude shafin neman tallafin Naira biliyan 110 daga asusun tallafawa matasa (NYIF) mutane 80,000 sun nemi tallafin
  • Gwamnatin tarayya ta ce za ta jajirce wajen nuna adalci da rikon gaskiya wajen zaben wadanda za su ci gajiyar wannan tallafin
  • A cewar ministar ci gaban matasa, Dakta Jamila Bio Ibrahim, manufar shirin NYIF shi ne tallafawa matasa 'yan kasuwa da jari

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Gwamnatin tarayya ta ce ta karbi bukatar mutane 80,000 a cikin sa’o’i 72 da bude shafin neman tallafin Naira biliyan 110 daga asusun tallafawa matasa (NYIF).

Gwamnati ta ce dandazon da aka yi na neman tallafin tun a tashin farko ya nuna irin shauki da sha'awar da matasan Najeriya ke da shi na samun tallafin kudaden.

Kara karanta wannan

A hakura da zanga zanga: Gwamnati za ta fara biyan matasa alawus na N50000 duk wata

Matasa 80,000 sun nemi tallafin N110bn na shirin NYIF awa 72 da bude shafin
Ministar ci gaban matasa, Jamila Bio Ibrahim ta ce matasa 80,000 sun nemi tallafin N110bn. Hoto: @fmydNG
Asali: Twitter

Matasa 80,000 sun nemi tallafin N110bn

A cewar gwamnatin, za a ba matasa tallafin Naira biliyan 110 ne domin su bunkasa sana'o'insu da kuma magance matsalar tattalin arzikinsu, inji rahoton The Nation.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ministar ci gaban matasa Dakta Jamila Bio Ibrahim ce ta sanar da hakan a wani taro da masu ruwa da tsaki na yankin Arewa ta tsakiya a Abuja.

Ministar ta ce ma’aikatar za ta ci gaba da jajircewa wajen tabbatar da yin adalci da riko da gaskiya wajen zaben wadanda za su ci gajiyar wannan tallafin.

Manufar shirin tallafawa matasa na NYIF

Jaridar Tribune ta ruwaito Dakta Jamila ta yi nuni da cewa:

"Domin habaka tasirin shirin, an sake fasalinsa ta yadda zai mayar da hankali kan manyan kasuwancin da ake da su tare da ƙirƙirar wasu sababbi da za su samar da ayyuka miliyan biyu a cikin shekaru uku.

Kara karanta wannan

Abubuwan sani dangane da zanga zangar da za a yi a Najeriya

“Asusun NYIF zai samar da tsarin ba matasa 'yan kasuwa da masu kirkire-kirkire tallafin kudade domin ci ba matasanmu kwarin guiwa da damar samun su ci gaba a sana’o’insu."

Ministar ci gaban matasan ta ce gwamnatin Shugaba Bola Tinubu ta ba da muhimmanci sosai wajen karfafa hadin gwiwa da masu ruwa da tsaki domin cimma nasarar manufofinta.

Tinubu ya fadi lokacin ba matasa tallafi

A wani labarin, mun ruwaito cewa shugaban kasa Bola Tinubu ya roki matasan Najeriya da su kauracewa zanga-zanga yayin da ya ce nan gaba kadan za a basu tallafin N110bn.

Ministar ci gaban matasa, Dakta Jamila Bio Ibrahim ce ta bayyana hakan yayin ganawa da kungiyar matasan MBYC a birnin Abuja inda ta ce matasan za su sami tallafin karkashin NYIF.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.