FG ta bayar da sabon bayani kan shirin bayar da tallafin kudi ga matasa (kalli lambobin wayar kowani yanki)

FG ta bayar da sabon bayani kan shirin bayar da tallafin kudi ga matasa (kalli lambobin wayar kowani yanki)

- Fadar Shugaban kasa ta bukaci wadanda suka nemi kudin tallafi na NYIF da su nemi karin bayani daga yankinsu

- Bashir Ahmad, mai ba Shugaban kasa Buhari shawara a kan shafin sadarwa, ya bayyana hakan a ranar Alhamis, 21 ga watan Janairu ta wani wallafa da yayi a Twitter

- Ahmad ya bayar da lambobin wayan jagororin shirin a fadin yankunan kasar

Gwamnatin tarayya ta aika wani sako ga dukkan matasan da suka nemi shiga shirin bayar da tallafi ga matasa na Najeriya wato Nigerian Youth Investment Fund (NYIF) gabannin sakin sunaye.

Legit.ng ta rahoto cewa fadar Shugaban kasa a wani wallafa da hadimin Shugaban kasa Muhammadu Buhari na musamman kan sadarwa, Bashir Ahmad, yayi a twitter a ranar Alhamis, 21 ga watan Janairu, ya bukaci wadanda suka nemi shiga tsarin da su tuntubi jagororin yankinsu.

KU KARANTA KUMA: COVID-19: NCDC ta rahoto karin mutum 1,964 sun harbu da cutar

FG ta bayar da sabon bayani kan shirin bayar da tallafin kudi ga matasa (kalli lambobin wayar kowani yanki)
FG ta bayar da sabon bayani kan shirin bayar da tallafin kudi ga matasa (kalli lambobin wayar kowani yanki) Hoto: @MBuhari
Asali: Twitter

Fadar Shugaban kasa ta bukaci matasan da suka nemi tallafin da su samu cikakken bayani kan tsarin daga wajen jagororinsu.

Yankunan sun hada da kudu maso kudu, arewa maso gabas, arewa maso yamma, kudu maso yamma, arewa ta tsakiya da kudu maso gabas.

Ya wallafa:

“Ka nemi kudin tallafi na matasan Najeriya? Don samun bayani abun dogari kan tsarin, tuntubi wadannan lambobi 07047024251 – kudu maso kudu; 07047598382 – arewa maso gabas; 08181127180 – arewa maso yamma; 08152947812 – kudu maso yamma; 07087792103 – arewa ta tsakiya; 07053820081 – kudu maso gabas."

KU KARANTA KUMA: CCB, Hukumar INEC za su je kotu a kan kadarorin Mahmoud Yakubu

A wani labarin kuma, a ranar Alhamis, 21 ga watan Junairu, 2021, shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya yi magana game da bashin da gwamnatinsa ta ke yawan ci.

Jaridar Daily Trust ta rahoto shugaban kasar ya na cewa gwamnatin tarayya ta buge da neman bashi ne a sakamakon karancin kudi a halin yanzu.

A cewar shugaba Buhari, ana samun gibi a kasafin kudin Najeriya saboda yadda kudin shigar da gwamnatin tarayya ta ke samu ya sauka na wasu shekaru.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng