Gwamnan APC Ya Ce ba Zai Iya Biyan Sabon Mafi Karancin Albashi ba, ya Fadi Dalili

Gwamnan APC Ya Ce ba Zai Iya Biyan Sabon Mafi Karancin Albashi ba, ya Fadi Dalili

  • Gwamnan Gombe, Inuwa Yahaya ya ce ba zai iya biyan ma'aikatan jiharsa sabon mafi karancin albashin N70,000 ba
  • Gwamnan ya yi nuni da cewa ko tsohon albashin N30,000 sai jihar ta yi da kyar ake iya biya sakamakon matsin tattalin arziki
  • A hannu daya, shugaban kungiyar gwamnonin Arewa ya ce har yanzu Gombe ba ta karbi tirela 20 na shinkafa daga Tinubu ba

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Gombe - A ranar Talata, gwamnan jihar Gombe, Inuwa Yahaya, ya fadi cewa gwamnatinsa ba za ta iya biyan sabon mafi karancin albashi na N70,000 ba.

Gwamna Inuwa Yahaya, ya yi magana a wani taro da shugabannin kwadago, kungiyoyin farar hula, da ’yan kasuwa gabanin zanga-zangar da za a yi a fadin kasar.

Kara karanta wannan

Ana tsaka da kuka da mulkin APC, 'yan majalisa 3 a Arewa sun sauya sheka zuwa daga PDP

Gwamna Inuwa Yahaya ya yi magana kan sabon mafi karancin albashi
Gwamnan Gombe, Inuwa Yahaya ya ce ba zai iya biyan sabon albashi na N70000 ba. Hoto: @governor_gombe
Asali: Facebook

"Ba zan iya biyan N70000 ba" - Gwamna

Jaridar Leadership ta ruwaito Gwamna Inuwa ya koka kan cewa cewa jihar Gombe na daya daga cikin jihohin da ke karbar mafi karancin kaso daga gwamnatin tarayya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

“Ba zan iya biyan mafi karancin albashin N70,000 ba, kuma ina zargin wasu jihohi da dama suna cikin wannan mawuyacin halin.”

- Gwamna Inuwa Yahaya

Gwamnan, wanda shi ne shugaban kungiyar gwamnonin Arewa ya ce samun kudi kadan ya sa jihar na fuskantar kalubale wajen iya biyan ma'aikata albashinsu.

Gombe ba ta karbi tallafin shinkafa ba

Gwamnan ya yi nuni da cewa hatta mafi karancin albashin N30,000 da aka amince da shi a baya, gwamnoni da dama na shan wahala kafin su biya.

Ya jaddada cewa yanayin tattalin arzikin da ake ciki a halin yanzu yana kara zama kalubale ga jihohi wajen aiwatar da sabon tsarin albashi, inji rahoton jaridar Premium Times.

Kara karanta wannan

NYSC: Tinubu zai ƙarawa matasa masu bautar ƙasa alawus? Abu 3 da ya kamata ku sani

Gwamna Inuwa ya kuma ce har yanzu Gombe ba ta karbi tirela 20 na shinkafa da gwamnatin tarayya ke rabawa jihohi ba, da nufin rage radadin da ‘yan kasar ke ciki.

An karawa ma'aikatan Gombe albashi

A wani labarin, mun ruwaito cewa gwamnatin jihar Gombe ta amince da ƙara wa ma'aikatan jihar albashi domin rage masu radadin cire tallafin man fetur.

Gwamnatin jihar karkashin jagorancin Inuwa Yahaya ta amince da ƙara wa kowane ma'aikaci a kowane mataki N10,000 a albashinsa.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.