Gwamnatin jihar Gombe zata dawo biyan ƙarancin albashi nan kusa

Gwamnatin jihar Gombe zata dawo biyan ƙarancin albashi nan kusa

- Gwamnatin jihar Gombe ta sanar da cewa zata ci gaba da biyan mafi ƙarancin albashi

- Gwamnan jihar ya sanya hannu a kasafin kudin 2021 ciki har da mafi ƙarancin albashin

- Gwamnatin ta kuma rage kudin gudanar mulki daga 25% zuwa 10%

Jaridar Daily Trust ya ruwaito cewa, Gwamnatin jihar Gombe ta ce za ta ci gaba da biyan sabon mafi karancin albashi ga ma'aikatan gwamnati a jihar daga watan Janairun 2021.

Kwamishinan kudi da ci gaban tattalin arziki na jihar, Muhammad Gambo Magaji, ya bayyana hakan yayin bayar da ragin kasafin kudin jihar na 2021 da Gwamna Inuwa Yahaya ya sanya hannu.

Gwamnatin jihar a watan Maris na shekarar 2020 ta dakatar da biyan N30,000 a matsayin mafi karancin albashi bayan ta biya na tsawon wata guda, tana mai bayyana dalilan raguwar kudaden shiga.

KU KARANTA: ‘Yan sanda sun cafke mutum 18 da ake zargi da tayar da tarzoma a Zamfara

Gwamnatin jahar Gombe zata dawo biyan ƙarancin albashi nan kusa
Gwamnatin jahar Gombe zata dawo biyan ƙarancin albashi nan kusa Hoto: Facebook/Daily Trust
Asali: Facebook

Magaji ya bayyana cewa kasafin kudin na 2021 ya kama sabon mafi karancin albashi, yana mai cewa shi ne dalilin da ya sa yawan ma'aikata a kasafin da aka amince ya tashi.

Ya kuma bayyana cewa don inganta jin dadin mazauna, an rage kudin gudanar da mulki zuwa kasa da kashi 10 cikin 100 na dukkan kasafin kudin, “sabanin tsohuwar gwamnatin da ta kashe kashi 25 cikin 100.”

KU KARANTA: Allurar rigakafin COVID-19: Damuwa kan Sayen ta, Adana ta da Gudanar da ita

A wani labarin, Gwamnatin jihar Gombe a ranar Laraba ta bayyana cewa an biya N873m a matsayin diyya ga masu filaye a jihar, Punch ta ruwaito.

Da yake bayyana hakan ga manema labarai bayan kammala taron zartarwar jihar wanda Gwamna Inuwa Yahaya ya jagoranta, kwamishinan yada labarai, Alhassan Ibrahim, ya ce asalin filin mallakar gwamnati ne, amma an biya kudin ne saboda dattakun gwamnan.

Ibrahim ya kara da cewa an yi hakan ne don amfanin jama'a, yana mai cewa hakan ya ta'allaka ne ga ci gaban jahar.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.