Karancin albashi: Gwamnatin Jahar Gombe ba za ta biya kananan hukumomin N30,000 ba
Gwamnatin jahar Gombe ta sanar da hukuncin da ta yanke game da sabuwar dokar karancin albashi, inda ta bayyana cewa ba za ta iya biyan ma’aikatan kananan hukumomi karancin albashin N30,000 ba.
Daily Trust ta ruwaito mataimakin gwamnan jahar, kuma shugaban kwamitin tattaunawa, Dakta Manassah Daniel Jatau ne ya bayyana haka a ranar Litinin, 2 ga watan Maris yayin da yake mika rahotonsa ga gwamnan jahar, Inuwa Yahaya.
KU KARANTA: Kisan kiyashi a Kaduna: El-Rufai ya lashi takobin share yan bindiga daga doron kasa
Tun a watan Disambar 2019 ne gwamnan ya kafa kwamitin mutane 15 a karkashin jagorancin mataimakin gwamnan da za su tattauna game da yiwuwar biyan N30,000 a matsayin sabon karancin albashi tare da duba gyare gyaren da za’a yi.
Mataimakin gwamnan ya ce bayan gudanar da nazari cikin natsuwa game da kudaden da jahar take samu, tare da duba halin da lalitar jahar take ciki, ma’aikatan gwamnatin jaha ne kadai za su iya samun karancin albashin N30,000.
Don haka yace kwamitinsu ta yanke shawarar lura da kudaden kananan hukumomin jahar 11 na tswon shekara daya don duba karfinsu, domin duba yiwuwar ko za su iya biya a nan gaba ko kuwa.
“A halin da ake ciki kananan hukumomin jahar Gombe 11 ba za su iya biyan albashin N30,000 ba har sai karfin tattalin arzikinsu ya bunkasa, kuma kudaden shigarsu sun karu, a yanzu ma’aikatan gwamnatin jaha ne kadai za su samu wannan kari.” Inji shi.
A jawabinsa, Gwamna Yahaya ya yaba da kokarin da kwamitin ta yi tare da cikakken rahoton da ta samar, amma ya ce gwamnatinsa za ta yi duk mai yiwuwa don tabbatar da kananan hukumomin jahar 11 sun fara biyan karancin albashin zuwa gaba.
A wani labarin kuma, gwamnan jahar Kaduna, Nasir Ahmad El-Rufai ya yi alkawarin share duk wasu yan bindiga dake jahar Kaduna daga doron kasa biyo bayan wani mummunan hari da suka kai a ranar Lahadi inda suka kashe mutane 51.
Miyagun yan bindiga sun kai mummunar hari a ranar Lahadi, 1 ga watan Maris inda suka kashe mutane da dama a kananan hukumomin Igabi da Giwa, sa’annan suka kona gidaje da motoci da dama.
Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa
ko a http://twitter.com/legitnghausa
KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com
Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa
Asali: Legit.ng