Zanga Zanga: NYSC Ta Soke CDS a Watan Agusta, Ta Aika Sako ga ’Yan Bautar Kasa
- Hukumar NYSC ta sanar da dakatar da dukkanin wasu ayyuka na masu yiwa kasa hidima na watan Agusta a fadin kasar nan
- An dage shirin tantancewa da hidimtawa al’umma na wata-wata (CDS) ga mambobin NYSC saboda zanga-zangar da ake shirin yi
- Hukumar NYSC ta bayyana cewa za a sanar da ranar da 'yan bautar kasar za su ci gaba da yin shirin CDS din nan gaba kadan
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja - Hukumar NYSC ta dage shirin tantancewa da yiwa al'umma hidima na wata-wata (CDS) ga 'yan bautar kasa saboda shirin gudanar da zanga-zanga a fadin kasar.
A ranar 1 zuwa 10 ga watan Agusta ne matasa suka shirya gudanar da zanga-zangar adawa da tsadar rayuwa da kuma matsalar tattalin arziki.
NYSC ta aika sako ga 'yan bautar kasa
Bayanin hakan na kunshe ne a cikin wata takarda da aka aika zuwa ga shugabannin NYSC na jihohi, jami'an kananan hukumomi (LGIs), da jami'an shiyya (ZI), inji rahoton The Nation.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Takardar ta bayyana cewa NYSC ba ta lamuncewa masu yi wa kasa hidima shiga zanga-zangar da ka iya haifar da tabarbarewar doka da oda a kasar ba.
"Ana sanar da dukkanin masu yi wa kasa hidima cewa an dakatar da tantancewa da ayyukan CDS na wata-wata har sai an fitar da sanarwar dawowar shirin."
Zanga-zanga: NYSC ta gargadi matasa
A baya Legit Hausa ta rahoto cewa hukumar NYSC ta gargadi ‘yan bautar kasa kan shiga zanga-zangar da aka shirya yi a fadin kasar a ranakun 1 zuwa 10 ga watan Agusta.
Yetunde Baderinwa, kodinetan hukumar na jihar Legas, ya ce duk wani dan bautar kasa da aka kama yana gudanar da zanga-zanga, za a hukunta shi kamar yadda dokar NYSC ta gindaya.
A cewar Baderinwa, shirin na NYSC an yi shi ne domin hada kan ‘yan Najeriya kuma 'yan bautar da ke shiga zanga-zangar za su yi hannun riga da manufar hukumar ta NYSC.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng