Bankwana da Tsadar Fetur, Gwamnati ta Dauki Mataki 1 na Tallafawa Matatar Man Dangote

Bankwana da Tsadar Fetur, Gwamnati ta Dauki Mataki 1 na Tallafawa Matatar Man Dangote

  • Majalisar zartaswa ta tarayya ta amince da bukatar Shugaba Tinubu na sayar da danyen mai ga matatar Dangote a kudin Naira
  • FEC ta ce ganguna 450,000 da za a yi amfani da ita a cikin gida za a ba da ta a Naira ga matatun Najeriya, inda za a fara da matatar Dangote
  • An ce Tinubu ya dauki wannan matakin ne domin rage kudin waje da kasar ke kashewa tare da daidaita farashin fetur, dizal da sauransu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Majalisar zartarwa ta tarayya (FEC) ta umarci kamfanin NNPCL da ya fara sayar da danyen mai ga matatar Dangote da sauran matataun cikin gida a kudin Naira.

Kara karanta wannan

Muna tare da Dangote: 'Yan Najeriya sun kafe, sun ce dole gwamnati ta biyawa Dangote bukata

Shugaban hukumar FIRS, Zack Adedeji ya bayyana hakan bayan taron FEC da Shugaba Bola Tinubu ya jagoranta a ranar Litinin, inda ya ce an daina amfani da dala a cinikin.

Tinubu ya yi magana akan sayarwa Dangote danyen mai a kudin Najeriya
Gwamnatin Najeriya za ta fara sayarwa Dangote danyen mai a Naira. Hoto: @officialABAT, @AlikoDangote
Asali: UGC

Tinubu ya ba NNPC umarni kan Dangote

Zack Adedeji ya bayyana cewa an dauki wannan matakin ne domin rage kudin waje da kasar ke kashewa tare da daidaita farashin fetur, dizal da sauransu, inji rahoton Channels.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Shugaban na FIRS ya ce majalisar zartarwar ta ba kamfanin NNPCL umarnin fara aiwatar da wannan tsarin domin bunkasa samar da mai a cikin kasar.

Hakazalika, Mista Adedeji ya ce gwamnatin Tinubu ta ba da umarnin cewa cinikin tataccen man da Dangote zai sayarwa 'yan kasuwa zai kasance a Naira ba dalar Amurka ba.

"Matatar Dangote za ta zama ta farko" - Onanuga

Kara karanta wannan

NNPC ya aika sako ga ƴan Najeriya yayin da gidajen mai suka fadi sabon farashin fetur

Mai ba shugaban kasa shawara na musamman kan yada labarai, Bayo Onanuga, ya tabbatar da hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar a shafinsa na X.

Bayo Onanuga, ya ce FEC ta amince da sayar da gangana 450,000 da ake son a yi amfani da ita a cikin gida a farashin Naira ga matatun man Najeriya, ta hanyar amfani da matatar man Dangote a matsayin gwaji.

“Bankin Afrexim da sauran bankuna na cikin gida Najeriya ne za su aiwatar da kasuwanci tsakanin Dangote da NNPC. Nan gaba kadan za a sanar da kimar musayar kudin."

Matatar Dangote: 'Yan kasuwa sun magantu

A wani labarin, mun ruwaito cewa kungiyar yan kasuwa masu dillancin man fetur (IPMAN) ta bayyana babbar matsalar da za a fuskanta daga matatar man Dangote.

Kungiyar IPMAN ta bayyana cewa ba za ta iya sayen man fetur daga matatar Dangote ba saboda farashin zai kasance da tsada, amma ta ba da mafita a kan hakan.

Kara karanta wannan

Sauki zai zo nan kusa: Siminti zai sauka, BUA ya gano hanyar sauke farashi kayansa a Najeriya

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.