Dangote zai samar da lita miliyan 65 na mai da iskar gas a kullum daga matatar man fetirinsa

Dangote zai samar da lita miliyan 65 na mai da iskar gas a kullum daga matatar man fetirinsa

Katafariyar matatar mai da hamshakin attajiri, Alhaji Aliko Dangote ya gina a jahar Legas zata samar da man fetir, iskar gas, man jirage, da kalanzir da suka kai lita miliyan sittin da biyar da dubu dari hudu (65.4m Litres), a kullu yaumin.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito daraktan tsare tsare da manyan ayyuka na kamfanin, Devakumar Edwin ne ya bayyana a ranar Lahadi, inda yace an gina matatar man fetirin ta yadda zata iya tace danyen mai na Najeriya da na kasashen waje a tare da samar da duk abinda ake bukata daga cikinsu cikin sauki.

KU KARANTA: Wata sabuwa inji yan caca: An baiwa dalibai lasisin shan sigari don fahimtar darasi

Dangote zai samar da lita miliyan 65 na mai da iskar gas a kullum daga matatar man fetirinsa
Matatar mai
Asali: UGC

Edwin yace manufar kamfanin shine malale duk fadin Najeriya da isashshen man fetir, kalanzir da iskar gas, ta yadda yan kasa zasu samu yadda suke so har ma a fitar kasashen waje, ana sa ran hakan zai kara ma Najeriya matsayi a jerin kasashen dake fitar da tataccen man fetir.

“Aikin zai samar da ayyuka ga dubun dubatan matasan Najeriya kai tsaye da kuma a kaikaice, tare da habbaka tattalin arzikin Najeriya, haka zalika zai janyo kwararru zuwa Najeriya da zasu horas da yan kasa akan ilimin kimiyyar man fetir na zamani” Inji shi.

Bugu da kari a yanzu haka kamfanin na gina katafaren kamfanin sarrafa taki a Najeriya, wanda babu kamar a yankin yammacin Afirka kwata, da zai samar da tan miliyan 3 na taki a shekara guda.

Mista Edwin ya cigaba da fadin kamfanin zai samar da isashshen canjin kudaden kasashen waje kamar su dala ga gwamnatin Najeriya ko kuma babban bankin Najeriya, tare da samar da karin adadin manoman urea.

Daga karshe yace kamfanin ta fara tattara matasan yankin da matatar man take don taimaka musu da tallafin dogaro da kai, ta hanyar koya musu sana’o’in hannu daban daban, domin cin gajiyar duk wata dama da zata samu a gaba.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel