Mayakan Boko Haram Sun Farmaki Ofishin ’Yan Sanda, Sun Kashe Jami’ai da Sace Makamai

Mayakan Boko Haram Sun Farmaki Ofishin ’Yan Sanda, Sun Kashe Jami’ai da Sace Makamai

  • Rahotanni sun bayyana cewa mayakan Boko Haram ne sun kai hari ofishin ‘yan sanda na Jakana da ke Konduga a jihar Borno
  • An ce mayakan Boko Haram din sun kashe jami'an 'yan sanda da wata mata tare da kuma kwashe mayakamai da alburusai
  • Shugaban karamar hukumar Konduga, Honarabul Abbas Ali Abari, ya tabbatar da faruwar harin ga manema labarai

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Borno - Wasu ‘yan ta’adda da ake kyautata zaton ‘yan Boko Haram ne sun kai hari ofishin ‘yan sanda na Jakana da ke karamar hukumar Konduga a jihar Borno.

An ce mayakan Boko Haram din sun kashe jami'an 'yan sanda da wata mata tare da kuma kwashe mayakamai da alburusai.

Kara karanta wannan

'Yan Najeriya da suka kwashe shekara 24 a gidan yari ba tare da laifi ba sun samu tallafi

Mayakan Boko Haram sun farmaki ofishin 'yan sandan Borno
'Yan ta'adda da ake zaton mayakan Boko Haram ne sun kashe jami'an 'yan sanda a Borno. Hoto: Legit.ng
Asali: Original

A cewar majiyoyin tsaro, maharan sun kuma kona motocin sintiri biyu da babur guda na 'yan sandan, kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

'Yan Boko Haram sun farmaki 'yan sanda

An tattaro cewa maharan da suka yi wa jami’an tsaro tsinke, sun isa ofishin ‘yan sandan ne da misalin karfe 1:00 na dare inda suka yi artabu da jami’an har zuwa karfe 3:00 na dare.

"Sun yi galaba a kan jami'an, kuma suka shiga ofishin 'yan sanda suka yi awon gaba da makamai da alburusai tare da lalata motocin sintiri 2.
“Daya daga cikin motocin na ‘yan sanda ne, daya kuma na ‘yan kungiyar rundunar tsaron hadin guiwa ne (CJTF).”

- Inji wata majiya.

Ciyaman ya tabbatar da kai harin

Shugaban karamar hukumar Konduga, Honarabul Abbas Ali Abari, ya tabbatar wa manema labarai harin, inda ya yi alkawarin bayar da cikakken bayani da zarar ya samu.

Kara karanta wannan

Kwara: Miyagun 'yan bindiga sun farmaki masu ibada, 'yan sanda sun kai daukin gaggawa

Kokarin tattaunawa da jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar Borno, Nahun Kenneth, ya ci tura saboda bai amsa kiran waya ko sakon kar-ta-kwana ba.

Jaridar Vanguard ta ruwaito cewa Jakana, wadda ke kan titin Damaturu zuwa Maiduguri, tana da tazarar kilomita 45 daga Maiduguri, babban birnin jihar Borno.

Tubabbun Boko Haram sun kai hari Borno

A wani labarin, mun ruwaito cewa wasu da ake kyautata zaton ‘yan ta’addan Boko Haram ne da suka tuba sun sake daukar makamai yayin da suka farmaki jami'an tsaro a jihar Borno.

An ce tubabbun 'yan Boko Haram din sanye da kakin sojoji sun mamaye Kasuwar Fara a Maiduguri inda suka fatattaki jami'an hukumomin NCS da NDLEA.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.